Ba Buhari bane mafi tsufan shugaba a Afrika, zai iya shugabanci har gaba da 2019 – Dan'uwan Shugaba

Ba Buhari bane mafi tsufan shugaba a Afrika, zai iya shugabanci har gaba da 2019 – Dan'uwan Shugaba

- Malam Adnan Na-Habu, wani daga yanuwan shugaba Muhammadu Buhari kuma mai magana da yawun iyalan shugaban ya ce shugaban nada daman cigaba da mulki har gaba da 2019

- Da yawa daga yan Najeriya, musamman yan adawa suna fakewa da shekarunsa don zagon kasa ga wa gwamnatinsa a tunkarar shekarar 2019

Na-Habu ya jajirce da cewa shekarunsa basu da alaka da yanayin shugabancinsa a yayinda yake nuna cewa akwai shugabanni dayawa a africa da suka fisa tsufa.

A jawabansa daga NAIJ.com, Na-Habu ya kore jita-jitar cewa yanayin lafityarsa na iya hanashi gudanarda shugabancin kasar najeriya.yace kada mutane su manta da cewa a hawansa ne aka fara farfado da ayyuka, misali wutar lantarki kasa take da 400 mega watts,amma duk kiyayyar makiyi ya san cewa dai karfin wutar ya karu.saboda dayawa daga guraren da suke watanni babu wuta yanzu suna samun wutar awanni shida zuwa Goma.

KU KARANTA: Dalilin da ya hana Shugaba Buhari halartar taron FEC – Lai Mohammed

bayan jefa masa tambayar lura da shekarunsa,shin kana ganin shugaban na iya tafi da lamarin mulkin yarda ya kamata', Na-Habu yace, na san dayawa daga yan Najeriya, musamman yan adawa suna fakewa da shekarunsa don zagon kasa ga wa gwamnatinsa a tunkarar shekarar 2019, Ni bana ganin hakan matsala ne kamar yanda bayani ya gabata. Akwai banbanci tsakanin shekaru da rashin lafiya.

Tsufa kam na iya hana mutum yin abu yarda ni da kai zamu yi, amma koma dai ya ake ciki mu mu'amalanceshi ta hanyar lura da abubuwan da yayi ba ta abinda zai iya ba ko zai kasa. domin lura da shekarunsa akwai dayawa daga shuwagabannin Afrika da suka girme masa kuma mulkinsu na tafiya yarda ya kamata."

sakamakon haka shekaru ba abu ne da zai hana shi yin abu yanda ya kamata ba. kuma yawancin maganganunnan ina kyautata zaton daga yan adawa suke fitowa. kuma abinda bazasu gane ba shine a zahiri babu abinda zai iya hanasa samun damar tsayawa takarar 2019.

Ku biyoma a facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa/

Ko a twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim

Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim

Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim
NAIJ.com
Mailfire view pixel