Binciken 'yan jam’iyyar APC ya tayar da kura sosai

Binciken 'yan jam’iyyar APC ya tayar da kura sosai

- Jami'an 'yan sanda sun ziyarci gidan kanin tsohon gwamnan jihar Kano Rabi'u Musa Kwankwanso da nufin bankado kudade da makamai

- A fadar ta Kwankwason akwai tsoron yiwuwar rikidewar yakin hancin ya zuwa tsohuwar siyasar gaba

- Mataimakin shugaban majalisar dattawa sanata Ike Ekweremadu ya ce ana shirin a tura makamai da kudade a gidansa

Na baya-bayan nan dai a cikin binciken na zaman tsohon gwamnan jihar Kano Rabi'u Musa Kwankwanso da ya samu ziyara ta jami'an 'yan sanda ya zuwa gidan kaninsa garin Madobi da ke jihar Kano da nufin bankado kudade da makamai da ake da tunanin tsohon gwamnan ya boye. Kwankwaso dai na zaman sanatan jam'iyyar APC mai mulki na 3 da ya fuskanci ziyara ta jami'an tsaron cikin sabon shiri na bankado kudade da makamai na gwamnatin ta Najeriya.

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, tun kafin shi, dama 'yan sandan sun ziyarci gidan tsohon gwamnan jihar Gombe sanata Danjuma Goje da kuma sanata Sabo na Kudu daga jihar Jigawa. Wannan abu dai daga dukkan alamu ya harzuka 'yan APC din da suka taka rawa wajen tabbatar da sauyi ga kasar, amma kuma ake kallon sauyin na neman wucewa da saninsu. Duk da cewar dai a fadar tsohon gwamnan na Kano 'yan sandan sun kare tare da cin karo da zomaye maimakon akwatunan kudi ko na makamai dai, sabon yanayin da ke zaman manufa ta gwamnatin APC na da bukatar taka tsan-tsan da ma sanin yakamata a fadar kwankwason.

KU KARANTA KUMA: Jam'iyyar ADC ta nemi Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya fito takarar shugaban kasa

To sai dai kuma ko bayan 'yan APC din dai, su ma 'yan jam'iyyar PDP da ke adawa a halin yanzu na taraddadi a fadar, mataimakin shugaban majalisar dattawan tarrayar ta Najeriya sanata Ike Ekweremadu da ya ce ana shirin a tura makamai da kudade a gidansa, zargin kuma da hukumar EFCC ta ce ya yi kama da mafarkin rana ga duk wanda ya ke takama da gaskiya cikin harkokinsa. To sai dai kuma a fada ta Kwankwason akwai tsoron yiwuwar rikidewar yakin hancin ya zuwa tsohuwar siyasar gaba, wanda a fadar Malam Garba Shehu da ke zaman kakaki na gwamnatin sabon yakin ba shi aboki balle makiyi sai dai kowa tasa ta fishe shi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga bidiyon inda wani dan jam'iyyar APC mai mulki ya ce jam'iyyar na iya fadi a zabe mai zuwa a 2019

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan maganin Kodin a cikin matasa

Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan maganin Kodin a cikin matasa

Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan Kodin a cikin matasa
NAIJ.com
Mailfire view pixel