CBN ta dage haramcin ba da kudin shigo da wasu kaya

CBN ta dage haramcin ba da kudin shigo da wasu kaya

- Babban Bankin Najeriya ya dage haramcin dai na ba wasu kananan 'yan kasuwa canjin dala don shigar da wasu kayayyaki daga waje

- Masana sun ce kananan masana'antu na fuskantar wahala wajen samun kayan aiki da dalolin da suke bukata

- Masana da dama sun ce taimaka wa kananan masana'antu zai bunkasa tattalin arzikin kasar

Babban Bankin Nijeriya CBN ya ɗage haramcin da ya sa na bai wa wasu ƙananan 'yan kasuwa canjin dala don shigar da wasu kayayyaki daga waje.

A cewar wani masanin tattalin arziƙi, Abubakar Aliyu, ya ce matakin dai zai rage wa ƙananan kamfanoni wahalhalu saboda za su iya samun canjin dala a farashi ƙasa da yadda bankunan kasuwancin ke ba su.

Masanin ya ce: ''Ƙananan masana'antu za su samu damar shigar da kayayyakin da za su taimaka musu wajen sarrafa abubuwan da suke samarwa a cikin gida”.

CBN ta dage haramcin ba da kudin shigo da wasu kaya

Masana da dama sun ce taimaka wa kananan masana'antu zai bunkasa tattalin arzikin kasar

Ya kuma ce ta hanyar bullo da tsare-tsare na gajere da matsakaicin zango, kasar za ta iya samun ci gaba kuma za a ga amfanun abin.

Kananan masana'antu suna fuskantar wahala wajen samun kayan aiki da dalolin da suke bukata don sayo kayan da suke sarrafa hajojinsu.

Masana da dama sun ce idan aka taimaka wa ƙananan masana'antu, da haka za su ci gaba da aiki, mutane za su samu aikin yi, kuma tattalin arziki zai bunƙasa.

KU KARANTA KUMA: Abin da na tattauna da Shugaban kasa-Gwamnan CBN

Abubakar Aliyu ya ce idan aka ci gaba da wannan tsari ba shakka Nijeriya zata amfana sosai, haka su ma jama'a, da shi kansa CBN.

A cewarsa, matakin zai kuma saukaka matsalar samun daidaituwar farashin dala, saboda ba lallai ne kuma sai masu masana'antu sun je kasuwar bayan fage ko kuma bankunan kasuwanci suna wahala ba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Hukumar EFCC ta gurfanar da tsohon babban daraktan NNPC Andrew Yakubu a kotu kan zargin cin hanci da rashawa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnati ta karrama wadanda suka bada gudummawa wajen habakar kasuwanci a 2016/2017

Gwamnati ta karrama wadanda suka bada gudummawa wajen habakar kasuwanci a 2016/2017

Gwamnati ta karrama wadanda suka bada gudummawa wajen habakar kasuwanci a 2016/2017
NAIJ.com
Mailfire view pixel