Kuma? Majalisar dattijai ta sake maidawa Buhari hannun agogo baya (Karanta)

Kuma? Majalisar dattijai ta sake maidawa Buhari hannun agogo baya (Karanta)

- Majalisar dattawa ta ba da tabbacin zuwa makon gobe za ta kammala tantance kasafin kudin bana ta tura ga shugaba Muhammadu Buhari don sanya hannu.

- Mataimakin shugaban majalisar dattawan Ike Ikweremadu ya baiyana haka a lokacin da ya jagoranci zaman majalisar.

NAIJ.com ta samu labarin Ekweremadu ya bukaci ‘yan Nijeriya ka da su shiga zullumi kan kasafin kudin don shugaban kwamitin kasafi na majalisar dattawan Danjuma Goje da na majalisar wakilai na kammala aiki a matakin karshe don gabatarwa zauren majalisar kasafin don mika shi ga fadar shugaban kasa.

A jiya ne dai, Majalisar Dattawa ta dakatar da gabatar da rahoton kasafin kudin bana wanda aka tsara kwamitin kudi na majalisar zai yi don amincewar zauren majalisar wanda kuma ake sa ran gabatar da shi ga Shugaban kasa don ya rattaba hannu.

Kuma? Majalisar dattijai ta sake maidawa Buhari hannun agogo baya (Karanta)

Kuma? Majalisar dattijai ta sake maidawa Buhari hannun agogo baya (Karanta)

Idan ba a manta ba, tun a watan Disamba na shekarar da ta gabata ne Shugaba Buhari ya turawa majalisar tarayya kasafin kudin don neman amincewarsu amma har yanzu ba su kammala aikin ba kuma a makon da ya gabata ne, Shugaban Zauren Majalisar Dattawa, Sanata Ahmed Lawan ya tabbatar da cewa a yau ne, za a mikawa Buhari Kasafin kudin.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin APC ta saki jerin hanyoyi da gadoji da ta kammala cikin shekaru 2 kacal

Gwamnatin APC ta saki jerin hanyoyi da gadoji da ta kammala cikin shekaru 2 kacal

Gwamnatin APC ta saki jerin hanyoyi da gadoji da ta kammala cikin shekaru 2 kacal
NAIJ.com
Mailfire view pixel