Jam'iyyar ADC ta nemi Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya fito takarar shugaban kasa

Jam'iyyar ADC ta nemi Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya fito takarar shugaban kasa

- Jam'iyyar ADC ta ce tabbasa irin su Sarki Sanusi ne kadai zasu iya gyara Najerya.

- Jam'iyyar ta mika kokon baranta ga Sarki Sanusi da ya fito takarar shugaban kasa a inuwar ta

- Jam'iyyar tace ita tuni ta dawo daga rakiyar Buhari, tace ta ammanar Sarki Sanusi ne zai iya ceton Najeriya

Shugaban Jam'iyyar ta African Democratic Congress (ADC), Cif Ralph Nwosu ne ya mika wannan kokon barar ga Sarkin na Kano a yayin hirarsa da jaridar Guadian.

NAIJ.com ta samu labarin a cewar sa, jam'iyyar APC bisa ga dukkan alamu ta bayyana ma jama'a karara cewar ba ta da maganin matsalolin Najeriya don haka ya zama dole a kauda ta a zaben 2019 mai zuwa.

Jam'iyyar ADC ta nemi Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya fito takarar shugaban kasa

Jam'iyyar ADC ta nemi Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya fito takarar shugaban kasa

KU KARANTA: Cutar Ebola zata iya dawowa a Najeriya

Shugaban na jam'iyya sai yace wannan ne yasa ya zama dole yan Najeriya su fito don neman wanda zai maye gurbin shugaba Buhari din a zabe mai zuwa.

Ya ci gaba da cewa rikicin rashin lafiyar shugaban kasa Muhammadu Buhari ma kadai ya isa ya sa yan Najeriya su tashi tsaye don ganin an yi wani canjin a shekara ta 2019.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad
NAIJ.com
Mailfire view pixel