To fa! Shugaban kasar Amurka Trump ya kunya Obama

To fa! Shugaban kasar Amurka Trump ya kunya Obama

- Majalisar wakilan Amruka da keda rinjayen yan Republican ta amince da kudirin soke shirin inshorar kiyon lafiya da gwamnatin shugaba Barack Obama ta samar

- Al’amarin da ke nuna soma sauye sauyen da shugaba Donald Trump ke son aiwatarwa akan manufofin gwamnatin da ta gabace shi.

Majalisar dokoki ta amince da kudirin soke dokar insharar ne a cikin gaggawa, bayan da wakilai 217 suka kada kuri’ar amincewa da manufar, a kan kuri’un wakilai 213, daukacin su kuma yan Democrat da wasu yan tsirari da Republican wadanda suka nuna rashin amincewarsu da soke shirin.

NAIJ.com ta fahimci cewa wannan dai na nuna cewa, shugaba Trump ya share rashin nasarar da ya cimma a ranar 24 ga watan maris din da ya gabata a lokacin karatun farko, sakamakon rashin samun jituwa tsakanin yan majalisar ta Rep masu rinjaye, duk kuwa da matsin lamba da suka fuskata, inda aka tilastawa repubilican da ta jaye kudirin na farko awa guda kafin soma zaben.

To fa! Shugaban kasar Amurka Trump ya kunya Obama

To fa! Shugaban kasar Amurka Trump ya kunya Obama

KU KARANTA: Likitoci daga waje 3 sun zo duba Buhari

Shugaban masu rinjaye na Repablican a majalisar dokokin Paul Ryan, ya ce amincewa da dokar na nini, da cika alkawarin da suka daukarwa amerikawa ne, tare da danganta tsohon shirin na Obamacare, da aka amince da shi a 2010, da zama batan bashira.

A lokacin da yake bayyana godiya ga shugaba Donald Trump kan rawar da ya taka wajen cimma wannan nasara Paul Ryan ya ce sun jima suna jiran wannan rana tsawon shekaru da suka gabata.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Taron Majalisar zartarwa na yau zai gudana a Ofishin Uwargidar shugaban kasa, shin menene dalili?

Taron Majalisar zartarwa na yau zai gudana a Ofishin Uwargidar shugaban kasa, shin menene dalili?

Taron Majalisar zartarwa na yau zai gudana a Ofishin Uwargidar shugaban kasa, shin menene dalili?
NAIJ.com
Mailfire view pixel