Hukumar jarabawar JAMB ta fitar da sakamakon jarabawar gwajin da tayi

Hukumar jarabawar JAMB ta fitar da sakamakon jarabawar gwajin da tayi

Hukumar jarabawar share fagen shiga manyan makaratun kasar nan JAMB ta bayyana sanarwar fitar da sakamakon jarabawar gwaji ta Mock da ta yi wa wasu daliban da za su zana jarabawar JAMB din ta bana.

Hukumar ta ce sama da dalibai 150,000 da suka zauna jarabawar za su iya zuwa shafin hukumar domin duba sakamakon da suka samu.

NAIJ.com ta samu labarin cewa har ila yau hukumar ta ce makin ba za ya yi wani tasiri a jarabawar JAMB din da za a fara gudanarwa a ranar 13 ga watan Mayun wanna shekarar ba.

Hukumar jarabawar JAMB ta fitar da sakamakon jarabawar gwajin da tayi

Hukumar jarabawar JAMB ta fitar da sakamakon jarabawar gwajin da tayi

KU KARANTA: Shekau yayi sabon Bidiyo

Sannan kuma sun bayyana cewa za a rufe shafin yin rijistar zauna jarabawar JAMB din a ranar Jumu'a 5 ga watan May da karfe 12am na dare.

Sun kuma bayyana cewa wajen dalibai miliyan 1.7 ne ake sa ran zauna jarabawar a santoci 633 da ta ware a duk fadin kasar nan.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59
NAIJ.com
Mailfire view pixel