Kasar Amurka tayi wa jihar nan ta Arewa sha-tara ta arziki (Karanta)

Kasar Amurka tayi wa jihar nan ta Arewa sha-tara ta arziki (Karanta)

- Kungiyar kula da cigaba na kasa da kasa na kasar Amurka USAID ta yi waji jihar Kogi sha-tara ta arziki

- Ta tallafa wa gwamnatin jihar Kogi da gidajen sauro sama da miliyan biyu domin rage yaduwar cutar zazzabin cizon sauro a jihar.

Darektan kungiyar Nancy Lowenthal ta dankawa gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello wannan gidajen sauron tare da wasu kudaden da ya kai dala miliyan 1.1 domin wayar da kan mutanen kananan hukumomi 21 dake jihar akan mahimancin amfani da gidajen sauron.

NAIJ.com ta tsinkayi cewa Gwamnan Yahaya ya gode wa USAID da irin wannan taimako da ta kawo jihar sannan yayi alkawarin ganin cewa jihar ta yi amfani dasu yadda ya kamata.

A wani labarin kuma, Majalisar dattawa ta ba da tabbacin zuwa makon gobe za ta kammala tantance kasafin kudin bana ta tura ga shugaba Muhammadu Buhari don sanya hannu.

Kasar Amurka tayi wa jihar nan ta Arewa sha-tara ta arziki (Karanta)

Kasar Amurka tayi wa jihar nan ta Arewa sha-tara ta arziki (Karanta)

KU KARANTA: Na gana da Buhari - Godwin Emefile

Mataimakin shugaban majalisar dattawan Ike Ikweremadu ya baiyana haka a lokacin da ya jagoranci zaman majalisar.

Ekweremadu ya bukaci ‘yan Nijeriya ka da su shiga zullumi kan kasafin kudin don shugaban kwamitin kasafi na majalisar dattawan Danjuma Goje da na majalisar wakilai na kammala aiki a matakin karshe don gabatarwa zauren majalisar kasafin don mika shi ga fadar shugaban kasa.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel