Dillalan motoci a jihar Kaduna sun banka ma motar Hukumar Kwastam wuta

Dillalan motoci a jihar Kaduna sun banka ma motar Hukumar Kwastam wuta

-Rikici ya kaure tsakanin jami'an hukumar kwatsam da dillalan motoci

-Matasan dillalan motocin sun babbaka moytar kwastam guda daya

Wasu fusatattun dillalai masu sana’ar sayar da motocin hawa a jihar Kaduna sun cinnawa wata motar hukumar shige da fice wuta biyo bayan wani samame da hukumar ta kai a wajen sana'arsu dake kan titin Isa Kaita a garin Kaduna.

Jaridar Rariya ta tattauna da wani da abin ya faru a idonshi mai suna Malam Saidu Mai jarida, kuma ya shaida cewar :

KU KARANTA: Muhimman abubuwa 4 da ka iya kada Buhari a zaben 2019

“Jami'an Kwastam din sun kai samame wajen 'yan motocin inda sukayi awon gaba da wasu motoci hudu wadanda suke zargin an shigo dasu ba bisa ka'ida ba.

Dillalan motoci a jihar Kaduna sun banka ma motar Hukumar Kwastam wuta

motar Hukumar Kwastam wuta

“Bayan wannan kuma suka sake dawowa inda suka sake kwashe ragowar motoci guda biyu dake wajen, lamarin daya tunzura dillalan motocin kenan suka bi bayansu har ya zuwa daidai mahadar shiga titin Rabah dake unguwar Sarki Kaduna.

Dillalan motoci a jihar Kaduna sun banka ma motar Hukumar Kwastam wuta

Motar Hukumar Kwastam

“Inda fitilar bada hannu ta tsayar dasu, amma motar Kwastam din da sauran motoci biyu da suka dauko sun samu wucewa, saura motar hukumar daya ta rage bata wuce ba dillalan motar suka dira kanta suka cinna mata wuta.” Inji majiyar NAIJ.com

Dillalan motoci a jihar Kaduna sun banka ma motar Hukumar Kwastam wuta

Motar Hukumar Kwastam

Sai dai a nasu bangaren, shugaban kungiyar dillalan motocin jihar Kaduna ya shaida cewa ba 'yan kungiyarsu bane suka yi wannan aika aika.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Dan Najeriya ya lashe kambun damben Duniya

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Alheri gadon barci: Halayyar kirki da wani mutumi ya nuna ma wata Zakanya ya sa sun shaƙu da juna, kalli hotunan su

NAIJ.com
Mailfire view pixel