Kwankwaso ya soki lamirin yansanda na kai farmaki gidan dan uwansa

Kwankwaso ya soki lamirin yansanda na kai farmaki gidan dan uwansa

-Tsohon dan takarar shugaban kasa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya soki yansanda dasu kai hari gidan kaninsa

-Kwankwaso yace yayi takaicin ace gwamnatin Buhari ke yi masa bita da kulli

Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya soki lamirin jami’an hukumar yansanda da suka kai farmaki gidan kaninsa dake Kano da nufin binciken makamai da kudaden sata da suke zargin an boye a gidan.

Kwankwaso ya bayyana haka ne cikin wata hira da yayi da gidan rediyon BBC a ranar Alhamis 4 ga watan Mayu, inda yayi zargin bita da kulli ake yi masa.

KU KARANTA: Magoya bayan Sule Lamido sun yi tururuwa wajen tarbarsa daga kurkuku (Hotuna)

“Jiya da safe muka samu labarin jami'an tsaro sun je gidan kanina a Kano da nufin bincike kan zargin da suke na cewa an boye motoci da makamai a gareji, inda suka kwashe a wanni suna bincike.

Kwankwaso ya soki lamirin yansanda na kai farmaki gidan dan uwansa

Kwankwaso

“Har sai da jami’an tsaro suka kama mai gadin gidan, suna yi masa barazana ya nuna musu inda aka boye motocin amma abin sha'awa ana bude garejin sai aka ga zomaye ne ake kiwo a ciki. Haka suka dinga bankade bankade, amma basu ga komai ba.

“Wannan abin takaici ne a kasa irin Nijeriya wadda mu da talakawa muka yi tsayin daka don ganin an samu canjin gwamnati, domin talakawa su ji dadi, amma sai gashi mun tsinci kanmu a cikin irin wannan yanayi.

"Da ace gwamnatin Jonathan ce ta yi min haka da ba zan damu ba, amma sai ga shi gwamnatin da muka wahala da ita ne take yi mana bita da kulli.” Kamar yadda majiyar NAIJ.com ta ruwaito.

Kwankwaso ya cigaba da nuna bacin ransa inda yake fadin “Ka ganni nan, bana kusanto da iyalaina da dangina cikin harkokin gwmanati, kanina yayi ritaya tun a loakcin da nake gwamna, amma kalli cin mutuncin da suka yi masa.”

Da aka tambaye shi ko yayi nadamar shiga APC, Kwankwaso yace “Zan bayyana ra’ayina a lokacin daya dace, amma dai gwamnati ta shiga taitayinta.”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

A binne shuwagabannin Najeriya, inji wani

Source: Hausa.naija.ng

Related news
In da ranka, ka sha kallo: Yadda wani mutumi ya ƙulla kyakkyawar abota da Zakanya (Hotuna)

In da ranka, ka sha kallo: Yadda wani mutumi ya ƙulla kyakkyawar abota da Zakanya (Hotuna)

Alheri gadon barci: Halayyar kirki da wani mutumi ya nuna ma wata Zakanya ya sa sun shaƙu da juna, kalli hotunan su
NAIJ.com
Mailfire view pixel