‘Kada kayi ƙasa a gwiwa’: Maitama Sule ya shawarci Buhari akan yaƙi da ɓarayi

‘Kada kayi ƙasa a gwiwa’: Maitama Sule ya shawarci Buhari akan yaƙi da ɓarayi

-Alhaji Yusuf Maitama Sule ya shawarci Buhari ya cigaba da yaki da rashawa

-Gwamna Ganduje yace martabar Najeriya ta dawo sakamakon kokarin Buhari

Dattijon Arewa, Alhaji Yusuf Maitama Sule, Dan masanin Kano ya shawarci shugaban kasa Muhammadu Buhari da kada ya kuskura ya ja da baya a yakin dayake yi da cin hanci da rashawa.

Maitama Sule ya bayyana haka ne a yayin kaddamar da tsarin yaki da rashawa a hukumar isar da sakonni, NIPOST a ranar Alhamis 4 ga watan Mayu a birnin Kano, kamar yadda jaridar Daily Trust ta dauko rahoto.

KU KARANTA: Magoya bayan Sule Lamido sun yi tururuwa wajen tarbarsa daga kurkuku (Hotuna)

“Ana samun rashawa a ko ina a Najeriya, don haka gwamnati ta dage wajen kwato kudaden al’umma daga hannun barayin gwamnati. Daga nan idan tag a dama ma ta sake su.” inji shi.

‘Kada kayi ƙasa a gwiwa’: Maitama Sule ya shawarci Buhari akan yaƙi da ɓarayi

Maitama Sule

Dayake nasa bayanin, majiyar NAIJ.com ta jiyo gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje yana fadin

“Sakamakon yaki da rashawa da shugaba Buhari yake yi, martabar Najeriya ya daukaka, kowa na sane da biliyoyin nairorin da gwamnatin Buhari take kwatowa tun bayan fara wannan yaki da rashawa.”

Daga karshe, shugaban hukumar karban koke koke da yaki da rashawa na jihar Kano, Muhiyi Magaji ya bayyana cewar suma a matakin jiha sun samu gagarumar nasara a yakin da suke yi da rashawa tun hawan gwamnatin gwamna Ganduje.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Yadda gwamnatin Buhari ta kama tsohon shugaban NNPC da satan kudi

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59
NAIJ.com
Mailfire view pixel