An kawo wasu Likitoci cikin Villa domin duba Shugaba Buhari

An kawo wasu Likitoci cikin Villa domin duba Shugaba Buhari

– An kawo wasu Likitoci daga kasar waje domin duba shugaban kasa

– Likitocin dai Turawa ne kuma an maida shugaban kasar zuwa wani daki

– Shugaban kasar na ta fama da rashin lafiya

Wasu Likitoci 3 sun shigo Najeriya domin duba lafiyar shugaba Buhari.

Daga cikin Likitocin na kasar Birtaniya akwai mace guda.

Jaridar Sahara Reporters ce dai ta fitar da wannan labari.

An kawo wasu Likitoci cikin Villa domin duba Shugaba Buhari

Shugaba Buhari bayan ya dawo daga jinya

NAIJ.com na samun labari game da rashin lafiyar shugaban kasa Buhari inda mu ke jin cewa wasu wasu Likitoci har 3 sun shigo kasar domin duba lafiyar shugaba Muhammadu Buhari wanda yanzu an yi makonni da dana ba a gani ba.

KU KARANTA: Tsofaffin Shugabannin kasa sun yanke shawara game da Buhari

An kawo wasu Likitoci cikin Villa domin duba Shugaba Buhari

Shugaba Buhari tare da Abba Kyari lokacin zai bar kasar

Likitocin kusan duk ‘Yan kasar Ingila ne kamar yadda shugaban kasar ya saba da zuwa kasar. Hukumar tsaro ta NIA ta maida shugaban kasar cikin wani daki na dabam inda za a duba sa. Jaridar tace wasu mukarraban shugaban sun hana a kai sa asibiti kasar waje.

Makon nan Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai yake cewa bai yi niyyar tsayawa takarar Gwamna ba shugaba Buhari ya matsa masa yace idan ya kara tilasta masa hakan za ayi a zabe mai zuwa.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Dangin Gwarzon Dan Najeriyar nan da ya ci gasar dambe

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Buhari ya amince a sayo jiragen ruwa don toshe kafofin barna da samar da tsaro a hanyoyin ruwa

Buhari ya amince a sayo jiragen ruwa don toshe kafofin barna da samar da tsaro a hanyoyin ruwa

Buhari ya amince a sayo jiragen ruwa don toshe kafofin barna da samar da tsaro a hanyoyin ruwa
NAIJ.com
Mailfire view pixel