Boko Haram: Abubakar Shekau ya fito a sabon bidiyo

Boko Haram: Abubakar Shekau ya fito a sabon bidiyo

– Shugaban kungiyar Boko Haram Shekau yace babu wani hari da aka kai masa

– A baya an rahoto cewa an jikkata shugaban kungiyar

– Kungiyar Boko Haram dai ta gagari kasar musamman a da can

A baya mun kawo cewa Sojojin Najeriya sun kai wani hari ga ‘Yan Boko Haram.

Inda har Shugaban Kungiyar Abubakar Shekau ya jikkata.

A wani sabon bidiyo Shekau yace karya ne.

Boko Haram: Abubakar Shekau ya fito a sabon bidiyo

Shugaban Boko Haram Shekau

Shugaban Kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau yace babu wani hari da aka kai masa a kusa da Dajin Sambisa inda ake ikirarin har ya samu rauni a wani sabon bidiyo da ya saki a jiya Alhamis da maraice.

KU KARANTA: Jami'ar tsaro ta auri Dan ta'addan ISIS

Boko Haram: Abubakar Shekau ya fito a sabon bidiyo

Abubakar Shekau a wani bidiyo

A da can NAIJ.com ta rahoto cewa Sojojin saman Najeriya sun kai wani hari a wani kauye da ke kusa da Garin Damboa inda aka raunata shugaban Kungiyar. Sai dai a sabon sakon da Shekau ya fitar ya musanya hakan yace yana nan kalau.

Dama dai Sojojin Najeriya da na Nahiyar sun saba ikirarin cewa har ma wai sun kashe Abubakar Shekau sai dai har yau yana nan da ran sa kamar yadda mu ka fada maku.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Yadda aka saki Jagoran Biyafara Kanu

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Canji! Gwamnatin shugaba Buhari zata sake ɗiban sabbin hafsoshin Yansanda

Canji! Gwamnatin shugaba Buhari zata sake ɗiban sabbin hafsoshin Yansanda

Canji! Gwamnatin shugaba Buhari zata sake ɗiban sabbin hafsoshin Yansanda
NAIJ.com
Mailfire view pixel