Kotu ta yankewa kansila da jami'in hukuncin zaman kurkuku akan laifin karkata buhun shinkafa 180 na yan gudun hijra a Borno

Kotu ta yankewa kansila da jami'in hukuncin zaman kurkuku akan laifin karkata buhun shinkafa 180 na yan gudun hijra a Borno

- Babban kotun tarayya ta yanze hukunci garkame ma’aikatan gwamnati 2 a gidan yari

-An kamasu da laifin karkata abincin yan sansanin gudun hijra

Wata babban kotun tarayya da ke Maiduguri ta yanke hukuncin zaman kurkuku na tsawon Shekara 1 da kuma taran N1m kan jami'an gwamnatin jihar Borno 2 kan laifin karkatar da buhun shinkafa 180 na yan gudun hijra.

Barayin sune Bulama Zangebe, kansila da Modu Bulama, Yan karamar hukumar Mafa.

Hukumar hana almundahana da yima tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC ta gurfanar da su ne kan laifin cuta da yaudara.

Game da karar, sun hada baki be da wani Shettima Maina, wani tsohon Shugaban karamar hukumar, wajen aikata laifin.

Kotu ta yankewa kansila da jami'in hukuncin zaman kurkuku akan laifin karkata buhun shinkafa 180 na yan gudun hijra a Borno

shinkafa

Maina Tuni yana hannun jami'an Sojin Najeriya akan laifin ajiye wani dan Boko Haram a gidan sa.

Zangebe da Bulama sun sayar da shinkafan N1.4 million. Kana kuma sun sake sayar da wani buhu 65, N585,000.

KU KARANTA: Soji sun kashe mataimakin Shekau

Alkalin kotun ya yanke hukuncin kwashe Shekara 1 a kurkuku da taran N1m. Hakazalika laifi na biyu ma hakan.

A karshe, alkalin yace zasu ci kurkukun ne a Jere.

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59
NAIJ.com
Mailfire view pixel