Jihar Benuwe ta haramta kiwon shanu a fadin jihar

Jihar Benuwe ta haramta kiwon shanu a fadin jihar

-Yan majalisan jihar Benuwe sun sanya dokar ta baci kan Fulani makiyaya

-Yanzu dai ana sauraron shin gwamnan zai rattaba hannu ko ko?

A yau Alhamis ne majalisan dokokin jihar Benuwe ta kaddamar da dokar haramta kiwon shanu a fadin jihar.

Shugaban kwamitin majalisan dokokin kan aikin noma, Mr. James Gbande, ne ya gabatar da wannan doka.

Yan majalisan sun tattauna akai Kuma sunyi ittifakin cewa wannan doka zai kawo karshen fadace-fadace tsakanin makiyaya da manoma.

Jihar Benuwe ta haramta kiwon shanu a fadin jihar

Jihar Benuwe ta haramta kiwon shanu a fadin jihar

Majalisan ta yanke cewa duk makiyayin da aka gani ya saba wannan doka zai ci gidan yarin Shekaru 5 da taran N1m.

Cewarsu: "Babu wanda aka amince yayi kiwo sabanin inda aka kebe musu.

“duk makiyayin da aka gani ya saba wannan doka zai ci gidan yarin Shekaru 5 da taran N1m.

KU KARANTA: Anyiwa Jonathan kaca-kaca

“Idan kuma dabbobin sukayi lalata ga kayan gona, za'a kiyasta kudin abinda aka lalata kuma a tilasta makiyayin ya biya.

“Tafiya da dabbobi haramun ne a jihar. Duk wanda aka kama zai kwashe Shekara 1 a kurkuku da taran N500,000.

“Duk wanda kuma aka kama ya Kora shanayen Jama'a, zai kwashe Shekara 5 a kurkuku da taran N100,000 kan kowani shanu.”

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim

Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim

Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim
NAIJ.com
Mailfire view pixel