Wutar lantarki yayi baya a Najeriya

Wutar lantarki yayi baya a Najeriya

– A halin da ake ciki wutar lantarkin da kasar nan ke samu ya ragu

– A da baya ana samun fiye da Mega-watt 4500 wuta

– Yanzu abin yayi kasa da haka

Wutar lantarki da aka samu a Najeriya ya ragu a yanzu haka.

Mun samu wannan bayani ne daga Jaridar Daily Trust.

Wuta kan karu da lokacin damina.

Wutar lantarki yayi baya a Najeriya

Lantarki ya zama kayan gabas Najeriya

NAIJ.com na da labarin cewa wutar da ake samu a Najeriya ta ragu a yanzu haka bayan da aka rasa mega watt sama da 420 a karshen watan jiya watau Afrilu. Kafin nan ku na labari cewa wutar lantarki da Najeriya ke samu ya haura Mega-watta 4500.

KU KARANTA: Chime yace APC za ta shawo kan matsalolin kasar nan

Wutar lantarki yayi baya a Najeriya

Ministan wutar lantarki Najeriya Raji Fashola

Yanzu abin da ake rabawa kasar dai shi ne mega watt 3598. Wasu lokuta a kan samu matsalar har ta kai na’urorin bada wutan su tsaida aiki gaba daya. A lokacin damina dai ana samun karuwar wuta saboda na’urorin da ake amfani da ruwa a Arewacin kasar.

Gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari tace cikin matsalolin da ake fama da su a Najeriya akwai rashin isassun gidajen zama, da wadataccen abinci da kuma sha’anin tsaro da ma wutar lantarki.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel