Boko Haram: An kashe mataimakin Shekau har lahira

Boko Haram: An kashe mataimakin Shekau har lahira

– Sojojin Najeriya sun kai wani hari ga ‘Yan Boko Haram

– Shugaban Kungiyar Abubakar Shekau ya jikkata a harin

– Bugu da kari an kashe mataimakin shugaban kungiyar

Kwanan NAIJ.com ta rahoto cewa an kai wani mummun hari ga Shekau inda ya samu rauni.

An kuma kashe wani babban Mataimakin sa da ake kira Malam Abba.

Har wa yau an kashe wani babban Mayakin ‘Yan ta’addan a harin.

Boko Haram: An kashe mataimakin Shekau har lahira

An kashe mataimakin Shekau

Ba shakka ku na sane cewa ana kan nasara wajen murkushe ‘Yan Kungiyar Boko Haram abin ya kai har Abubakar Shekau ya sha da kyar a wani hari da Sojojin saman Najeriya su ka kai a wani kauye da ke kusa da Garin Damboa.

KU KARANTA: Sojoji sun kashe manyan 'Yan Boko Haram

Boko Haram: An kashe mataimakin Shekau har lahira

Shugaban Boko Haram Abubakar Shekau

Muna da labarin cewa an kai hari inda aka jikkata shugaban Boko Haram Abubakar Shekau tare da kuma kashe wani babban Mataimakin sa Abba Mustafa. Daily Trust tace akwai wani wani babban Dan kungiyar da aka samu kashewa a harin.

A baya dai Sojojin Najeriya da waje ba sau daya ko biyu ba sun saba ikirarin cewa har ma wai an kashe Abubakar Shekau sai dai har yau yana nan da ran sa.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Wani Dan Damben Duniya Anthony Joshua

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile faruwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma

Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile faruwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma

Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile afkuwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma
NAIJ.com
Mailfire view pixel