Sarkin musulmi ya gargadi ‘yan Najeria

Sarkin musulmi ya gargadi ‘yan Najeria

- Alhaji Muhammadu Sa'ad Abubakar III wanda shi ne sarkin musulmi ya bukaci ‘yan Najeriya da su guje maimaitan yaki basasa a kasar

- Sultan ya jaddada cewa 'yan Nijeriya su zauna lafiya tare da juna cewa wani yakin basasa zai iya tarwatsa kasar

Sarkin musulmi Alhaji Muhammadu Sa'ad Abubakar III ya bukaci ‘yan Najeriya da su guje wa kura-kuran da ya kai ga yakin basasa Biyafara.

NAIJ.com ta ruwaito cewa Sultan ya yi wannan gargadin ne yayin da yake bayani a wajen taron bikin ranar sarakunan gargajiya da aka gudana a Jihar Ribas.

Sultan ya jaddada bukatar 'yan Nijeriya su zauna lafiya tare da juna cewa wani yakin basasa zai iya tsaga kasar.

Sarkin musulmi ya gargadi ‘yan Najeria

Sarkin musulmi Alhaji Muhammadu Sa'ad Abubakar III

Ya ce: "Najeriya na sama da shekaru 50 yanzu kuma ta yi yakin basasa. Dole ne mu gane cewa Najeriya ba zai iya tsira ga wani yakin basasa ba. Saboda haka, ya kamata mu guje maimaita irin wannan kuskuren da ya kai mu ga yakin basasa."

KU KARANTA KUMA: Muhimman abubuwa 4 da ka iya kada Buhari a zaben 2019

Ya yi kira da baban murya ga 'yan siyasa cewa su hada kai tare da sarakunan gargajiya don samu cigaba a kasar saboda sarakunan sun kasance a mulki kafin kirkiro kasar Najeriya.

Ya kuma bukaci sarakunan gargajiya a jihar Ribas su goyi bayan manufofin gwamnatin a kan ci gaba da zaman lafiya.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Sariki Sanusi ya shawarci shugabannin Najeriya da shugabanci na nagari a cikin wannan bidiyo

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim

Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim

Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim
NAIJ.com
Mailfire view pixel