Ciwon sankarau ta sake ballewa a jihar Katsina, akalla 8 sun hallaka

Ciwon sankarau ta sake ballewa a jihar Katsina, akalla 8 sun hallaka

-Sankarau ta sake fasa kai arewacin Najeriya kwanakin nan

-A jihar Katsina, akalla mutane 8 ne aka ruwaito sun rasa rayukansu

Ciwon sankarau wanda turawa suka sani da Cerebro Spinal Meningitis ya hallaka mutane 8 a kauyen Tsabu da ke karamar hukumar Mai'adua a jihar Katsina.

Diraktan asibitin Yara da ke karamar hukumar Mai'adua, Nasir Mani , ya tabbatar da hakan ga manema labarai.

Mani yace sabuwar ballewar cutan ya bayyana ne kwanaki 2 da suka gabata.

Yace an gano mutane 16 da cutan, amma 8 ne suka rigamu gidan gaskiya.

Game da cewarsa, sauran mutanen na babban asibitin Mai'adua domin kula na kwarai.

Yace hadin kan likitocin jihar da karamar hukumar ya taimaka kwarai wajen dakile matsalan.

Ciwon sankarau ta sake ballewa a jihar Katsina, akalla 8 sun hallaka

Ciwon sankarau ta sake ballewa a jihar Katsina, akalla 8 sun hallaka

Ina kira ga mutanen mu su taimaki kansu wajen yin rigakafin da ke gudana domin kare kansu daga cutan.

“ Munada wurare na musamman a kauyuka na rigakafin,"

KU KARANTA: Gwamnatin jihar Zamfara zata dauki malamai aiki

Mani ya yabawa kungiyar Medicines San Frontiers (Doctors Without Borders) akan rawar da taka wajen dakile matsalan.

Yayi kira ga mutanen yankin su bi umurnin tsaro na bacci a dakuna masu iska.

Kana kuma ya basu shawara su kai karan duk wani abin lura cibiyar kiwon lafiyan da ke kusa.

https://web.facebook.com/naijcomhausa/?ref=bookmarks

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59
NAIJ.com
Mailfire view pixel