Bamu san lokacin da za'a gabatar da kasafin kudin 2017 ba - Kakakin majalisan dattawa, Abdullahi Sabi

Bamu san lokacin da za'a gabatar da kasafin kudin 2017 ba - Kakakin majalisan dattawa, Abdullahi Sabi

-Majalisar dattawa tace bata shirya kasafin kudin Najeriya ba

-Ana wata 5 yanu cikin shekarar 2017 amma ba’a gabatar da kasafin kudin kasa ba

Shugaban kwamitin majalisan dattawa kan yada labarai da hulda da Jama'a, Sanata Abdullahi Sabi ya bayyana cewa bai san lokacin da za'a gabatar da kasafin kudin kasa na shekaran nan ba.

Jama'an Najeriya na sa ran za'a gabatar da kasafin kudin kasan yau, Alhamis ne amma Sanata Abdullahi Sabi ya ce gaskiya ba'a shirya ba.

“Suna harhadawa Kuma suna bi a hankali saboda tabbatar da cewa komai yayi dai-dai."

Bamu san lokacin da za'a gabatar da kasafin kudin 2017 ba - Kakakin majalisan dattawa, Abdullahi Sabi

Bamu san lokacin da za'a gabatar da kasafin kudin 2017 ba - Kakakin majalisan dattawa, Abdullahi Sabi

“Wannan shine aiki mafi wuya saboda sai an duba sosai. Idan kuka lura yau, Baku ga Shugaban kwamitin kasafin kudin kasa ba a majalisa. Suna iyakan kokarinsu akai."

KU KARANTA: An bada belin Sule Lamido

“Ban san lokacin da za'a gabatar da shi ba. Abinda na sani shine suna kokari wajen tabbatar da cewa komai yayi dai-dai. Abu ne wanda idan mukayi kuskure daya, zai shafi dukkan takardar.

“Babu dan siyasan da ba zai so abubuwa su cigaba ba saboda mune abin zai fi shafan. Mun fi kowa damuwa kuma muna son abubuwa suyi kyau."

https://web.facebook.com/naijcomhausa/?ref=bookmarks

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila
NAIJ.com
Mailfire view pixel