Jami'an hukumar yan sanda sun far ma gidan Kwankwaso a Kano

Jami'an hukumar yan sanda sun far ma gidan Kwankwaso a Kano

- Sifeto janar na Yan sanda IGP Idris Ibrahim ya aika jami'ansa bincikar gidan Kwankwaso

- Jami'an sun dira gidan da tsakar ranan Laraba

Jami'ai na musamman daga ofishin Sifeto janar na Yan sanda, IGP Idris Ibrahim, ta kai farmaki gidan dan uwan Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, Lawan Musa Kwankwaso a jihar Kano.

Majiya ta bayyanawa jaridar Vanguard cewa " Jami'an tsaro sun afka cikin gidan ranan Laraba kuma an tabbatar da zuwansu a ofishin yan sandan Sharada.

“Yanada alaka da wani kasuwanci da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso yayi da sunan kaninsa.

“Jami'an sun dira gisan da tsakar Rana kuma suka gudanar da bincike sosai na kimanin sa'o'i 3 " .

Jami'an hukumar yan sanda sun far ma gidan Kwankwaso a Kano

Jami'an hukumar yan sanda sun far ma gidan Kwankwaso a Kano

An tattaro cewa Lawan Musa Kwankwaso ya bayar da hadin kai wajen binciken.

Duk da cewan ba'a bayyana abinda aka gano daga gidan ba, majiya ta ce an samu nasara.

KU KARANTA: An bada belin Umaru Naso da mai gidansa Mu'azu Aliyu

Amma, kakakin hukumar yan sandan jihar Kano, DSP Magaji Musa Majia, yace ba ofishinsu ta kai harin ba saboda haka ba zai iya magana akai ba.

“Babu ruwan mu da wannan bincike, bamuda alaka da harin."

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila
NAIJ.com
Mailfire view pixel