Badakalar Diezani: Na amince na karba cin hancin N70m - Jami'in INEC

Badakalar Diezani: Na amince na karba cin hancin N70m - Jami'in INEC

- Wani jami'in INEC yayi amanna da karban cin hancin magudin zabe

- Tuni ya salwantar da kudin ta hanyar tara kadarori

Wani jami'in hukumar gudanar da zabe na kasa Mai zaman Kanta wato INEC, Yisa olanrewaju, yayi amanna da cewa ya amsa N70,050,000.00 daga cikin N23billion da Diezani Allison-Madueke ta bayar domin magudin zaben 2015.

Hukumar Hana almundahana da yima tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC ta gurfanar da shi ne tare da Christian Nwosu da Tijani Inda Bashir akan zargin laifuka 6 na rashawan N264, 880, 000.00 a gaban Jastis M.B. Idris na babban kotun tarayya da ke Ikoyin jihar Legas.

Lauyan EFCC, Rotimi Oyedepo, ya bayyana wa kotu cewa Adedoyin ya anshi N28million daga cikin N70,050,000.00 da suka karba ta hannun Bashir.

Badakalar Diezani: Na amince na karba cin hancin N70m - Jami'in INEC

Badakalar Diezani: Na amince na karba cin hancin N70m - Jami'in INEC

Oyedepo ya kara da cewa hukumar EFCC ta gano kadarar N23m da kudi N5m a asusun bankin Adedoyin.

KU KARANTA: Kamfanoni 5 da Babachir yayi amfani da su wajen badakala

Amma, Adedoyin ya bukaci hukumar EFCC cewa zai biya taran N10m.

A shari'ar alkali Jastis Idris, ya amince da taran da akaci Adedoyin na biyan kudin ga hukumar EFCC.

https://web.facebook.com/naijcomhausa/?ref=bookmarks

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile afkuwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma

NAIJ.com
Mailfire view pixel