Aukuwar yanzu: An bada belin tsohon gwamna Sule Lamido bayan tsareshi da kwanaki 4

Aukuwar yanzu: An bada belin tsohon gwamna Sule Lamido bayan tsareshi da kwanaki 4

- Ikenna Ekpunobi, ya ja matuka a kotu akan kar a bada belin Lamido

- Alkalin Shari'a, Muhammad Lamin, ya kore dukkan tuhumar da akwa lamido akan rashin dalili

Kotun shari'a a Dutse ta baiwa tsohon gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido beli akan tatanceshi da tayi .

Mai tuhumar sa a kotun, Ikenna Ekpunobi, ya ja matuka akan kar a bada belin Lamido domin yana iya zama barazana ga zaman lafiyar jihar.

Alkalin Shari'a, Muhammad Lamin, bai yarda yabi wannan shawarar ba a fadar, NAIJ.com.

Mr. Lamin kuma bai yarda da rahoton yansanda dake nuna yunkurin yan zanga-zanga da magoya bayan tsohon gwamnan ke shirin yi ba.

A yunkurin kariya ga Lamido, Felix John, ya nuna cewa Lamido ba abin zargi banea zahiri face sai an tabbatarda hakan da hujja.

Aukuwar yanzu: An bada belin tsohon gwamna Sule Lamido bayan tsareshi da kwanaki 4

Sule Lamido, tsohon gwamnan jihar Jigawa

Ya kara da cewa tuhumar da ake masa rubutu ne kawai ba tareda hujja da zata goyi bayan hakan ba, Lamido,a matsayinsa na tsohon gwamna ya cancanci beli.

NAIJ.com tace Alkali mai shari'a ya zartar da bada belin Lamido daga tuhumar da ake yi masa.yace ” babu wani takamaiman kwakkwaran dalili da kotu zata iya dogaro dashi a tuhumar saboda haka baza'a hana belinsa ba. ''

An kama Lamido ne a ranar lahadi a gidansa na Kano kuma bincike yakai har Jigawa,babu wani abin tuhuma da aka samu taredashi lokacin a duka gidajen.

ya fuskanci shari'a ne a talata akan yunkurin tada tarzoma da ake zargin magoya bayansa ke iya yi a zaben kananan hukumomin jihar dake tafe. wannan ne dalilin tsareshi har izuwa yau Alhamis,ya musa dukkan tuhumar da ake masa ,kuma Jam'iyyarsa ta PDP sun nuna cewa wanna aikin jam'iyyar ada ce wato APC.

Ku biyomu a facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa/

ko a twitter : https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Taron Majalisar zartarwa na yau zai gudana a Ofishin Uwargidar shugaban kasa, shin menene dalili?

Taron Majalisar zartarwa na yau zai gudana a Ofishin Uwargidar shugaban kasa, shin menene dalili?

Taron Majalisar zartarwa na yau zai gudana a Ofishin Uwargidar shugaban kasa, shin menene dalili?
NAIJ.com
Mailfire view pixel