Siyasar Najeriya: Shin waye zai iya maye takalmin Shugaban Buhari a zaben 2019 in ya fasa tsaya wa takara?

Siyasar Najeriya: Shin waye zai iya maye takalmin Shugaban Buhari a zaben 2019 in ya fasa tsaya wa takara?

- Masana siyasar kasar nan na ganin yiwuwar maimaita dambarwar da ta faru a shekaru na mulkin tsohon shugaba marigayi Umaru Yar'Adua, ganin irin nuku-nuku da boye boye da makusantar shugaban kasa Muhammadu Buhari keyi game da lafiyarsa

- Hotuna da ke yawo a gari a nuni da cewa lallai shugaban yana jin jiki, duk da cewa yana wuri da ya kamata ace mutum ya sami kulawa ta lafiya mafi inganci.

- Haduwar tsofin shuwagabanni irin su Obasanjo da Abdulsalami da Babangida na nuni da lallai akwai damuwa a kan batun lafiyar shugaban, da ma makomar qasar nan, tun ma kafin a tunkari zabuka masu zuwa, nan da qasa da shekaru biyu.

Ganin yadda ta kaya a shekaru takwas da suka wuce, inda komai ya tsaya chak, saboda batun lafiyar mutum daya, masu fada aji na qasarnan, na ganin wannan karon, ya kamata a tari abun da wuri, kafin ace har sai an fara zanga-zanga a tituna domin sanin me shugaban da jama'a suka zaba ke ciki.

Su dai makusanta shugaban, sun nuna zuzuta batun kawai ake yi, amma masu sharhi na ganin tuni har daama ta sake budawa masu neman takara fara baje kolinsu a babban mataki na shugabancin kasar nan.

Jiga-jigai irinsu Atiku Abubakar, Sule Lamido, Rabi'u Kwankwaso da sauran tsofin gwamnoni, tuni sun fara rawa mai kamar tsalle domin a fara qirgawa da su a lissafin sabon zubi. Shi kuma Gwamna mai ci a Kaduna Mallam Nasir El-Rufai yace baya da niyyar takarar wannan kujera mai qarfi, a hirarsa ta baya-bayan nan.

Ga dukkan alamu dai, akwai yiwuwar shugaba Buhari bazai nemi takara ba, domin ya samu ya huta, amma kuma akwai alamun bazai yi murabus ba har sai ya kammala shekaru hudun da ya kamata yayi. Kallo dai ya koma sama, magoya baya na masa fatan alheri, maqiya na fatan sharri, ya danganta wacce addu'a ce Allah zai karba, ko irin makomar Umaru Yaradua, sanda yana Gwamna, ko kuma makomar sa sanda yana shugaban kasa.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnati ta karrama wadanda suka bada gudummawa wajen habakar kasuwanci a 2016/2017

Gwamnati ta karrama wadanda suka bada gudummawa wajen habakar kasuwanci a 2016/2017

Gwamnati ta karrama wadanda suka bada gudummawa wajen habakar kasuwanci a 2016/2017
NAIJ.com
Mailfire view pixel