Shugaba Buhari zai sake tafiya ƙasar waje don duba lafiyarsa

Shugaba Buhari zai sake tafiya ƙasar waje don duba lafiyarsa

-Hadimar shugaban kasa Lauretta Onochie ta tabbatar da tafiyar shugaba Buhari don a duba lafiyarsa

-Onochie tace zai tafi ne kadai idan likitocinsa sun bukaci yin hakan

Fadar shugaban kasa ta tabbatar da shirin shugaban kasa Muhammadu Buhari na komawa kasar waje don a sake duba lafiyarsa idan lokacin yin hakan yayi.

Hadimar shugaban kasa, Lauretta Onochie ce ta bayyana haka a shafin ta na kafar sadarwar zamani, Tweeter a ranar Alhamis 4 ga watan Mayu.

KU KARANTA: Buhari zai warware nan bada daɗewa ba – inji jigo a PDP

Onochie tace duk kururuwan yan adawa ba zai tunzura shugaban kasa fita kasar waje ba, har sai likitocinsa sun bukaci hakan. Onochie ta bayyana wannan ne a matsayin raddi ga kalaman da wani shugaban kungiyar kare hakkin bil adama Adetokunbo Mumuni yayi a wani gidan talabijin akan rashin lafiyar shugaban kasar.

Shugaba Buhari zai sake yin tafiya ƙasar waje don duba lafiyarsa

Bayanin Onochie

Onochi tayi mamakin yadda Mumuni ke magana akan rashin lafiyar shugaban kasar duk da cewa baya kusa da shugaban kasar balle ma ya san halin da shugaban ke ciki, don haka ta shawarci yan Najeriya da suyi watsi da shi.

Shugaba Buhari zai sake yin tafiya ƙasar waje don duba lafiyarsa

Bayanin Onochi

A ranar Laraba 3 ga watan Mayu NAIJ.com ta ruwaito shugaban kasa Muhammadu Buhari bai samu daman halartan taron majalisar zartarwa ba, hakan ya sanya mataimakinsa farfesa Yemi Osinbajo jagorantar zaman.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Menene gaskiya rashin lafiyar Buhari, kalla

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59
NAIJ.com
Mailfire view pixel