Muhimman abubuwa 4 da ka iya kada Buhari a zaben 2019

Muhimman abubuwa 4 da ka iya kada Buhari a zaben 2019

-Tsohon kwamishinan yansanda ya koka kan abubuwan dake ci ma Buhari tuwo a kwarya

-Yaki da cin hanci da rashawa na daya daga cikin manyan matsalolin kasar nan, inji Abubakar Tsav

Tsohon kwamishinan yansandan jihar Legas, Abubakar Tsav yace akwai wasu muhimman abubuwa guda hudu da zasu iya kasa shugaban kasa a zaben 2019 idan ya nemi kara tsayawa takara.

Tsav ya bayyana haka ne cikin wani hira da yayi da jaridar ‘The Sun’, inda ya bayyana cewa shugaba Buhari ya jajirce wajen gyaran kasar nan tun bayan hawansa mulki.

KU KARANTA: Ya ɗaure matarsa a jikin Janareta da ankwa tun safe har yamma

Sai dai Tsav ya shawarci Buhari akan wasu abubuwa guda 4 dayake ganin zasu ci masa tuwa a kwarya, NAIJ.com ta kawo muku jerin abubuwan:

Muhimman abubuwa 4 da ka iya kada Buhari a zaben 2019

Abubakar Tsav

1- Yaki da cin hanci

Abubakar Tsav abinda ya bayyana shine cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ne kadai ke yaki da cin hanci da rashawa da gaske.

“Buhari yazo da kyakkyawan niyyar gyaran kasar nan, kuma yana dagewa, amma fa yaki da rashawa da yake yi baya samun goyon bayan majalisar dokokin Najeriya. Kuma har yanzu ba’a kama manyan barayi ba.”

2- Matsalar shafaffu da mai

Abubakar Tsav yace yan gaban goshin shugaban kasa sun mamaye komai a gwamnati, suke tafiyar da mulkin kasar.

“Ana zargin akwai wasu shafaffu da mai a fadar shugaban kasa, suma wadannan zasu iya kawo mai tasgaro a 2019, amma ina da yakinin Buhari zai yi maganin su.” inji Tsav.

3- Majalisun dokoki

Abubakar Tsav yace majalisun dokokin kasar nan suna bai wa Buhari ciwon kai musamman wajen tafiyar da kasar yadda ya kamata.

“A gani na, bai samu wasu muhimman nasarori ba. Amma ba laifinsa bane, saboda majalisun dokokin kasar nan na yi masa zagon kasa.” Inji shi.

4- Nuna Aminci da yarda

Shugaba Buhari ya aminta da mukarrabansa sosai, yasa baya ganin laifinsu, inji Tsav, don haka ya bada shawarar “Akwai amintattun yan Najeriya da dama, kuma kwararru da zasu iya aiki da Buhari don kawo canjin da muke nema.”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kalli ra'ayin jama'a kan tattalin arzikin kasa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59
NAIJ.com
Mailfire view pixel