Hukunci da kotu ta yanka ma abokin tsohon ministan man fetur (Diezani Madueke) na magudin zaben 2015

Hukunci da kotu ta yanka ma abokin tsohon ministan man fetur (Diezani Madueke) na magudin zaben 2015

- Alkali Mohammed Idris ya kaso Yisa Adedoyin domin samun N70,050,000

- Ana zarginsu da karbi N264.88 miliyan cin hanci a ranar 27 ga watan Maris, 2015

- Amma, alkali Idris ya ƙi rokon yarjejeniya da ya shiga tare da hukumar EFCC

- An amince a cikin rokon cewa, Adedoyin zai bari filinsa wanda ya auna 100ft da 100

Babbar Kotun Tarayya a jihar Legas jiya ta kaso wani ma'aikaci na hukumar zabe (INEC) domin ya karbi N70 miliyan, cin hanci daga tsohon Ministan man fetur Mrs. Diezani Alison-Madueke don magudin sakamakon zaben janar na shekarar 2015.

NAIJ.com ya tara cewa, alkali Mohammed Idris ya kaso Yisa Adedoyin domin samun N70,050,000 bayan ya amsa laifin wani caji da an gyara.

Hukumar Laifukan tattalin arzikin (EFCC) sun sake gurfanar da shi tare da Christian Nwosu da kuma Tijani Inda Bashir.

KU KARANTA: An bankado wata kungiyar da ke saye da sayarwar kodar mutane

Ana zarginsu da karbi N264.88 miliyan cin hanci a ranar 27 ga watan Maris, 2015 daga tsohon ministan kafin a yi zabe. Nwosu ya amsa laifin cajin da aka yi mishi kaso saboda laifin karbar N30 miliyan na rashawa.

Ana zargin wasu hukumar INEC da karba N264.88 miliyan cin hanci daga tsohon Ministan man fetur Mrs. Diezani Alison-Madueke don magudin sakamakon zaben janar na shekarar 2015

Ana zargin wasu hukumar INEC da karba N264.88 miliyan cin hanci daga tsohon Ministan man fetur Mrs. Diezani Alison-Madueke don magudin sakamakon zaben janar na shekarar 2015

Amma, alkali Idris ya ƙi rokon yarjejeniya da ya shiga tare da hukumar EFCC wanda aka yi a kan biyan N500,000 da kuma barin dukiya da ya samu ta amfani da kudin.

Alkalin ya ce Nwosu ya yarda a yanka mishi wani babban hukunci, wanda ya hada da biyan miliyan N10, ko ya canza roko. Lokacin aka sake gurfanar da su jiya, Nwosu ya canza roko zuwa cewa bai da laifi.

KU KARANTA: Wani mutum yayi ma matarsa ɗaurin kazar kuku a jikin Janareta tsawon yini guda

Lauyan la'anta Mista Rotimi Oyedepo ya bukaci kotun ta hukunta Adedoyin a cikin ra'ayi na rokonsa kuma kotu ta yarda da rokon yarjejeniyar da suka shiga da hukumar tun rana 2 ga watan Mayu.

Kotu ta amince a cikin rokon cewa, Adedoyin zai bari filinsa wanda ya auna 100ft da 100 a hanyar Taoheed, ƙauyen Budo-Osho, karamar hukumar Ilorin ta Kudu a jihar Kwara.

Alkali ya daga jin maganan na aikace-aikacen bayar da belin na Nwosu zuwa 15 ga watan Mayu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Wannan NAIJ.com bidiyo na nuna ma'aikatan hukumar INEC a kotu don zargin cin hanci da rashawa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Za’a sake ɗiban wasu sabbin hafsoshin rundunar Yansanda – Gwamnatin tarayya

Za’a sake ɗiban wasu sabbin hafsoshin rundunar Yansanda – Gwamnatin tarayya

Canji! Gwamnatin shugaba Buhari zata sake ɗiban sabbin hafsoshin Yansanda
NAIJ.com
Mailfire view pixel