Da dumi-dumi: Sojoji sun takaita yunkurin kunar bakin waken da wasu yan mata Maiduguri, mutum 3 sun rasa rayukansu.

Da dumi-dumi: Sojoji sun takaita yunkurin kunar bakin waken da wasu yan mata Maiduguri, mutum 3 sun rasa rayukansu.

- Yan matan uku ne daure da bama-bamai a jikinsu sukayi yunkurin kai harin a Maiduguri,, wani babban birnin jihar Borno

- Duk da kokarin takaita hare-haren, mutum uku tareda jami'in tsaro daya ne suka rasa rayukansu

Yunkurin harin da wasu yan mata uku sukayi yunkurin kaiwa ya auku ne a daren laraba a Maiduguri A cewar mai magana da yawun National Emergency Management Authority, Abdulkadir Ibrahim: "Yan matan uku na dauke da bama-baman ne a daure jikinsu a yayin da ya fadi daga jikinsu a yunkurin nasu."

Jami'in tsaro Ibrahim yace, ina daga cikin wadanda suka tinkari yan matan uku masu nufatar hare-haren.

A wani Jawabin nasa: “A daren jiya (Laraba, 3 ga watan Mayu a misalin karfe 10:05 na dare, yan matan uku sun nufaci kai harin ne wa madakatar sojoji da ake kira 'Guantanamo' a hanyar Muna garage.

KU KARANTA : ALBISHIRINKU: Janaral sojin kasa guda 2 sun tsere daga harin Boko Haram

“An hangosu ne tareda harbesu a yayinda suke kokarin shiga gurin , a sannan ne bamabaman suka tashi dasu tareda jami'in tsaro daya.''

Ibrahim ya kara da cewa ma'aikatan lura da hadari da sun mika gawarwakinsu wa asibitin kwararru Jihar Borno.

Ku biyomu a facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa/

Ko twitter : https://twitter.com/naijcomhausa

Bidiyon yadda za'a hallaka yan ta'addan Boko Haram

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Boko Haram: Sarkin Musulmi zai dauki nauyin marayu 200 a birnin Shehu

Boko Haram: Sarkin Musulmi zai dauki nauyin marayu 200 a birnin Shehu

Boko Haram: Sarkin Musulmi zai dauki nauyin marayu 200 a birnin Shehu
NAIJ.com
Mailfire view pixel