Boyi-boyi ya tarkata kayayyakin maigidansa ya ƙara ma wandonsa iska

Boyi-boyi ya tarkata kayayyakin maigidansa ya ƙara ma wandonsa iska

-Wani dan aikin gida ya tattara kayan maigidansa ya tsere

-Yansanda sun samu nasarar kama wannan mutum

Rundunar yansandan babban birnin tarayya reshen Gwarinpa ta kama wani dan aikin gida daya saci kayayyakin maigidansa da suka hada da waya, littafai da sauransu. Inji rahoton Daily Trust.

Wata majiya daga rundunar ta bayyana cewa sun kama dan aikin ne mai suna Albert bayan ya sace kayan maigidansa a gida mai lamba 44, CITEC Villa, Gwarinpa yayin dayake wanke masa mota.

KU KARANTA: Jerin kamfanunuwa 5 da suka baiwa Babachir cin hancin naira miliyan 507

Maigidan nasa ya shiga rudu ne bayan ya fahimci an yi masa awon gaba da dukiyansa daga cikin motar a lokacin daya zo daukar motar.

Boyi-boyi ya tarkata kayayyakin maigidansa ya ƙara ma wandonsa iska

Barawon waya

“Ya bar kayayyakin sa a cikin motar, amma bai gansu ba bayan yaron ya kammala wanke motar, daga nan ne sai ya kawo kara wajen yansanda” inji majiyar NAIJ.com.

DPO na yansandan Gwarinpa Nuruddeen Sabo ya tabbatar da faruwa lamarin, kuma yace wanda ake zargin ya amsa laifinsa, kuma ya dawo da dukkanin kayayyakin.

“Wanda ake zargi yana hannun mu, kuma zamu mika shi gaban kotu.” Inji DPO

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Dan Najeriya ya nemi gwamnati ta bashi iznin sata

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile afkuwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma

NAIJ.com
Mailfire view pixel