An bankado wata kungiyar da ke saye da sayarwar kodar mutane

An bankado wata kungiyar da ke saye da sayarwar kodar mutane

- Jami’an tsaro a Lahore da ke kasar Pakistan sun gano wata kungiya da ke saye da sayarwa na kodojin mutane.

- A wani sumame da suka kai wani gida, sun samu nasarar kama mutane 6, a ciki har da likitoci 2, wadanda aka kama suna aikin dasa koda akan wasu bakin haure guda biyu ‘yan kasar Oman.

Hukumin kasar sun ce sun gano cewa kungiyar ta na sayen kodar talakawan kasar wanda ke bukatar kudi, su sayar da su ga attajirai daga kasashen waje, musamman kasashen larabawa.

NAIJ.com ta samu labarin Kodar ta na tafiya ne akan farashin dala dubu 70 kowacce daya.

A karkashin dokar kasar Pakistan, ba a yarda a yi cinikayyar koda ba, sai dai idan mutum ya na bukatar dashe a asibiti, wani dan uwansa ya bayar.

An bankado wata kungiyar da ke saye da sayarwar kodar mutane

An bankado wata kungiyar da ke saye da sayarwar kodar mutane

KU KARANTA: Karin albashi zai rage cin hanci da rashawa

Toh sai dai tsananin talauci da wasu ‘yan kasar ke fuskanta ya ingiza su sayar da kodar su daya, domin samun kudade cikin gaggawa.

Yayin da wahalar da ake fuskanta wajen samun kodar ta sanya wasu shiga kasuwancin ta domin su samu abun yi.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Jirgin mata zalla na farko zai sauka Najeriya daga kasar Habasha

Jirgin mata zalla na farko zai sauka Najeriya daga kasar Habasha

Jirgin mata zalla na farko zai sauka Najeriya daga kasar Habasha
NAIJ.com
Mailfire view pixel