Ya ɗaure matarsa a jikin Janareta da ankwa tun safe har yamma

Ya ɗaure matarsa a jikin Janareta da ankwa tun safe har yamma

-Wani miji ya daure matarsa tamau a jikin Janareta na tsawon wuni guda

-Mijin yace yayi haka ne domin kare kansa daga sharrin matar tasa

Hukumar yansandan jihar Ogun ta kama wani mutum mai shekaru 37 mai suna Ifeanyi Ajaero kan zargin sa da lakada ma matarsa duka tare da daure ta a jikin Janareta na tsawon wuni daya a tsaye.

Wannan lamari ya faru ne a garin Sagamu na jihar Ogun, kuma hakan ya faru ne sakamakon sa’insa daya shiga tsakanin Ajaero da matarsa Obiageli.

KU KARANTA: Zamu cigaba da bincikar asusun masarautar Kano – Muhyi Magaji

Kaakakin rundunar yansandan jihar, Abimbola Opeyemi yace ya daure matar tasa ne da ankwa bayan ya lakada mata dan banzan duka, da azabtar da ita da horo mai tsanani. Kamar yadda NAIJ.com ta gano.

Ya ɗaure matarsa a jikin Janareta da ankwa tun safe har yamma

Uwargida Obiageli

Kaakakin yace “Makwabtan su ne suka kawo kara wajen yansanda, hakan ya sanya DPO dake yankin tura jami’an mu, inda suka ceto matar wanda tuni ta galabaita, tare da kama mijin nata.”

Mijin matar ya amsa laifinsa, inda ya bayyana cewa shi tsohon sojan ruwa ne, amma an kore shi daga aiki, kuma asali ma yana kare kansa daga sharrinta.

Ya ɗaure matarsa a jikin Janareta da ankwa tun safe har yamma

Mijin matar, Ajaero

Shima kwamishinan yansandan jihar Ahmed Iliyasu ya nuna bacin ransa da lamarin, sa’annan ya umarci a fara binciken wanda ake zargin.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ko kasan bayahuden daya tsaya ma shugaban Biafra? kalla

Source: Hausa.naija.ng

Related news
‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili

‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili

‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili
NAIJ.com
Mailfire view pixel