‘Yan Najeriya 300 ke jiran aiwatar musu da hunkuncin kisa a ketare

‘Yan Najeriya 300 ke jiran aiwatar musu da hunkuncin kisa a ketare

- Yanzu ‘yan Najeriya 300 ke jiran a aiwatar musu da hunkuncin kisa a kasashen waje

- Wata kungiyar kare hakkin bil Adama na neman a ceto ‘yan Najeriya da aka yanke wa hunkuncin kisa

- Kungiyar ta ce kimani ‘yan Najeriya 16,500 ne ke tsare a gidajen yarin duniya

Gwamnatin Najeriya ta ce abu ne mai wuya kasashen da suka yankewa 'yan kasar hukuncin kisa saboda safarar miyagun kwayoyi su amince da shirin musayar firsinoni da ita.

NAIJ.com ta ruwaito cewa ministan harkokin waje Geoffrey Onyeama ya bayyana haka, yayin ganawa da wata kungiyar kare hakkin bil Adama da ke neman ganin an ceto ‘yan Najeriya sama da 300 da yanzu haka ke jiran aiwatar musu da hunkuncin.

KU KARANTA KUMA: Da yiwuwan Buhari ya koma Landan wannan ranan - Majiya

Kungiyar ta bayyana cewar, yanzu akwai ‘yan kasar 120 a China da ke jiran aiwatar da hukuncin, bayan wasu 170 da ke kasashen Indonesia da Malaysia da Vietnam da Qatar da Daular larabawa da kuma Saudi Arabia.

Kungiyar ta kuma ce ‘yan Najeriya 16,500 ke tsare a gidajen yarin duniya.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Bayanai iyanlan wanda jami'in tsaro na farar hula ta tsare a cikin wannan bidiyo

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Boko Haram: Sarkin Musulmi zai dauki nauyin marayu 200 a birnin Shehu

Boko Haram: Sarkin Musulmi zai dauki nauyin marayu 200 a birnin Shehu

Boko Haram: Sarkin Musulmi zai dauki nauyin marayu 200 a birnin Shehu
NAIJ.com
Mailfire view pixel