Buhari zai warware nan bada daɗewa ba – inji jigo a PDP

Buhari zai warware nan bada daɗewa ba – inji jigo a PDP

-Wani Jigo a jam'iyyar PDP ya bayyana Buhari a matsayin ikon Allah ne

-Jigon yace shugaba Buhari zai samu lafiya nan bada dewa ba

Wani babban jigo a jam’iyyar adawa ta PDP kuma tsohon dan majalisa Alhaji Sa’idu Gumburawa ya bayyana tabbacinsa na cewa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari zata gyara kasar nan fiye da gwamnatocin baya.

Kamfanin dillancin labaru, NAN, ta ruwaito Gumburawa yana fadin hada a jihar Sakkwato, inda ya nuna gamsuwar sa da kamun ludayin shugaba Buhari, tare da bayyana yakinin zai kawo sauyi a kasar nan.

KU KARANTA: Zamu cigaba da bincikar asusun masarautar Kano – Muhyi Magaji

“Ina da yakinin yadda shugaba Buhari ke tafiyar da kasar nan, Najeriya zata gyaru. Misali, gwamnati ta samu nasara a yaki da yan ta’addan Boko Haram, sa’annan sauran matsalolin tsaro kamar garkuwa da mutane, satar shanu da fashi da makami sun samun kulawa.

Buhari zai warware nan bada daɗewa ba – inji jigo a PDP

Shugaba Buhari

“Ta bangaren tattalin arziki kuwa, ina ta tabbacin Najeriya zata fita da kangina karayar tattalin arziki nan gaba kadan, duk da cewa dai akwai sauran aiki.” Inji shi.

Gumburawa ya yaba ma shugaba Buhari ta yadda ya jajirce akan yaki da rashawa, inda ya bada shawarar a kama duk wani barawo, kuma a kwato kudaden al’umma.

Daga karshe NAIJ.com ta jiyo Gumburawa yana fadin “Buhari ikon Allah ne, kuma zamu canji a kasar nan.”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Sabon aikin da gwamnati ta baiwa yan Najeriya

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Mata masu juna 100 suka rasa rayukan su a jihar Zamfara - Ma'aikacin asibitin Gusau

Mata masu juna 100 suka rasa rayukan su a jihar Zamfara - Ma'aikacin asibitin Gusau

Mata masu juna 100 suka rasa rayukan su a jihar Zamfara - Ma'aikacin asibitin Gusau
NAIJ.com
Mailfire view pixel