Kotu ta tsare wani mutum dan shekara 25 saboda ya yi wa yaro dan shekara 5 fyade

Kotu ta tsare wani mutum dan shekara 25 saboda ya yi wa yaro dan shekara 5 fyade

- Wata kotun magistare a jahar Kano ta bayar da umarnin a tsare Sulaiman Bala mai shekaru 25 a gidan kasu a bisa tuhumar da ake masa na yi wa wani yaro mai shekaru 5 fyade.

- Lauyan mai kara, Rufa’i Inusa ya bayyanawa kotun cewa mahaifin yaron wanda ke zaune a kauyen Kofar Arewa a karamar hukumar Dawakin kudu na jahar Kano, shi ya kai kara ofishsin ‘yan sanda a ranar 22 ga watan Maris.

NAIJ.com ta samu labarin ya ce lamarin ya faru na a ranar 10 ga watan Maris a yayin da yaran ke kan hanyar sa na zuwa masallaci, a lokacin ne Bala ya yaudare shi zuwa wani shago, inda ya aikata aika aikar.

Lauyan ya ce daga bisani ne aka garzaya da yaran zuwa Asibitin Dawaki Kudu domin a yi masa magani.

Kotu ta tsare wani mutum dan shekara 25 saboda ya yi wa yaro dan shekara 5 fyade

Kotu ta tsare wani mutum dan shekara 25 saboda ya yi wa yaro dan shekara 5 fyade

A fadar sa, wannan laifi ya saba da sashe na 284 na kundin dokar Penal Code.

Sai dai Bala bai amsa laifin ba.

Alkalin kotun, mai shari’a Muhammad Jibril ya daga sauraran karar zuwa ranar 15 ga watan Mayu.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin APC ta saki jerin hanyoyi da gadoji da ta kammala cikin shekaru 2 kacal

Gwamnatin APC ta saki jerin hanyoyi da gadoji da ta kammala cikin shekaru 2 kacal

Gwamnatin APC ta saki jerin hanyoyi da gadoji da ta kammala cikin shekaru 2 kacal
NAIJ.com
Mailfire view pixel