Dillalan takin zamani suna bin gwamnatin tarayya bashin naira biliyan 29

Dillalan takin zamani suna bin gwamnatin tarayya bashin naira biliyan 29

- Dillalan takin zamani a Najeriya na kukan rashin biyansu naira miliyan 29 da suke bin gwamnati

- Dillalan sun ce bashin da suka ciwo daga bankuna na neman durkusar dasu

- Shugaban kungiyar dillalan y ace zasu iya rubuta a jaridu shugaba Buhari ya gani domin ya san ba'a taimakon manoma

Wasu dillalan takin zamani da suke bin gwamnatin tarayya zunzurutun kudi har na naira miliyan 29 sun yi dafifi a gaban ma'aikatar gona suna kukan cewa rashin biyansu ya sa jarinsu ya kusa durkushewa.

Dillalan da suka yi dafifi a gaban ma'aikatar gona sun samu kyakyawar karba daga sakataren ma'aikatar wanda ya yi masu albishirin cewa za'a duba batun.

Dillalan na cewa bashin da suka ciwo daga bankuna na neman durkusar dasu sakamakon rashin biyansu a kan kari bashin naira biliyan 29 da suke bin gwamnati. Akwai ma wani bashin na naira biliyan 10 tun bara na raba takin da wayar salula.

Dillalan takin zamani suna bin gwamnatin tarayya bashin naira biliyan 29

Dillalan da suka yi dafifi a gaban ma'aikatar gona

Kabiru Fara shugaban kungiyar dillalan yana mai cewa can baya ana gaya masu da baki za'a biya amma ba'a yi ba saboda haka su fito su bayyana masu da baki su kuma basu a rubuce shirin biyansu. Idan sun basu wa'adin biyan suka kuma wuce lokacin to duk abun da suka yi masu ruwansu, inji Kabiru Fara.

Dangane da abun da zasu yi idan ba'a biyasu ba, sai Kabiru Fara yace suna da zabi da dama. Akwai tafarkin siyasa kuma 'yan Najeriya sun gaji da yin alkawari babu cikawa. Zasu kuma rubuta a jaridu shugaba Buhari ya gani domin ya san ba'a taimakon manoma.

Suna kuma da zabin su je kotu su ce sai an biyasu dole. Yace amma tunda suna da dangantaka da ma'aikatar gona basa son lamarin ya kaiga shari'a.

KU KARANTA KUMA: Ana neman taimakon ‘yan Najeriya da gaggawa (Hotuna)

Alhaji Bello Abubakar Haliru Funtua mataimakin shugaban kungiyar manoman masara ta Najeriya ya ce taki yayi sauki a kasar saboda kafin wannan shirin da gwamnatin Buhari ta fito dashi sai da buhun taki daya ya kai naira 10,000.

NAIJ.com ta tattaro cewa daya daga dillalan na karfafa a cigaba da shirin koda ba'a kammala biyansu ba. Yace don tashi ba za'a yi zanga zanga ba. Bai yi aikin domin Audu Ogbe ya biyashi ba. Yana cewa idan gwamnatin mai adalci ce zata biyashi ko bai bi sawu ba. Ya ce kamar yadda talakawa suka shaida shugaba Buhari mai gaskiya ne duk ranar da ya farga suna bin gwamnati bashi za'a biyasu. Ya ce abun kunya ne a gwamnatin Buhari a ce talaka ya fito yana zanga zanga.

Yanzu dai gwamnatin Najeriya ta bada alkawarin biyan wasu kaso a cikin kudin nan da mako daya kamar yadda sakataren ma'aikatar gonan Bukar Hassan ya bada albishir.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kali yadda aka bada belin shugaban 'yan Biafara Nnamdi Kanu

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin APC ta saki jerin hanyoyi da gadoji da ta kammala cikin shekaru 2 kacal

Gwamnatin APC ta saki jerin hanyoyi da gadoji da ta kammala cikin shekaru 2 kacal

Gwamnatin APC ta saki jerin hanyoyi da gadoji da ta kammala cikin shekaru 2 kacal
NAIJ.com
Mailfire view pixel