Gwamnati ta duba halin da nakasassu ke ciki a Najeriya – Inji PDF

Gwamnati ta duba halin da nakasassu ke ciki a Najeriya – Inji PDF

- Kungiyoyin nakasassu a kasar nan na kukan ba’a tunawa dasu

- Shugaban sabuwar kungiyar nakasassun Najeriya ya ce, rikicin Boko haram ya maida wasu nakassasu

- Shugaban kungiyar ya kira gwamnatocin arewa da kuma kungiyoyin bada agaji da adinga tunawa dasu

Yayin da a Najeriya hukumomi ke tallafawa wadanda rikicin Boko Haram ya shafa, hadakar kungiyoyin nakasassu a kasar na kukan cewa ba’a tunawa dasu.

Rikicin Boko Haram dai ya lakume rayuka da dama, baya ga wasu dubban da aka tilastawa gudun hijira, kuma wani fannin da ba’a cika maida hankali ba shine halin da nakasassu suka shiga.

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari a wajen wani taron masu ruwa da tsaki na sabuwar kungiyar nakasassun Najeriya ta Progressive Disabled Forum, PDF, Kwamrad Ibrahim Alhassan Ganye, dake zama shugaban kungiyar a Najeriya, ya ce rikicin Boko haram ya maida wasu nakassasu, kuma abin takaici kawo yanzu hukumomi da kuma kungiyoyin agaji basa tunawa dasu a tallafin da ake badawa domin tada komadar al’ummomin da rikicin Boko Haram ya shafa.

Gwamnati ta duba halin da nakasassu ke ciki a Najeriya – Inji PDF

Kungiyar nakasassun Najeriya

Hakan yasa shugaban kungiyar ya mika kukansu ga gwamnatocin arewa da kuma kungiyoyin bada agaji da adinga tunawa dasu.

Ita kuwa Patience Briston, dake cikin wadanda rikicin Boko Haram ya nakasa biyo bayan tashin wani bom da ya rutsa da ita a garin Maiduguri, ta ce an maida su saniyar ware.

KU KARANTA KUMA: Rundunar Sojin Najeriya ta raunata Shekau, ta kuma kashe mataimakin sa

Kafin dai wannan rikici na Boko Haram gwamnatocin jihohin kan taimaka wajen kafa cibiyoyin koyon sana’a ga nakasassu shirin da a baya kwalliya ke biyan kudin sabulu.

Koda yake kullum dai gwamnatocin jihohi kan ce suna nasu kokari, to amma kuma sukan danganta rashin kudi da zama kanda –garkin halin da nakasassun ke ciki, kamar yadda gwamnan jihar Adamawa sanata Muhammadu Bindow Umaru Jibrilla ke cewa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kali bidiyon wasu yara da suka tsira daga hannun 'yan Boko Haram

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC

Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC

Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC
NAIJ.com
Mailfire view pixel