Jami’an fadar sarkin Kano sun bayyana gaban hukumar rashawa

Jami’an fadar sarkin Kano sun bayyana gaban hukumar rashawa

- Jami’an harkokin kudi na majalisar masarautar Kano sun bayyana gaban hukumar rashawa ta shiyar Kano

- Makon da ta gabata ne hukumar yaki da rashawa ta jihar Kano ta sanar da cewa za ta kaddamar da bincike kan harkokin masarautar

- Alhaji Bashir Wali ya ce mai martaba sarkin Kano Mohammadu Sunusi II ya gaji naira biliyan 1 da naira dubu 893,000

Jami’an harkokin kudi na majalisar masarautar Kano sun bayyana a hedikwatar hukumar yaki da rashawa ta jihar Kano, domin bada bahasi dangane da binciken zargin anyi ba dai-dai ba wajen sarrafa kudaden masarautar cikin shekaru 3 da suka gabata.

A makon jiya ne dai hukumar yaki da rashawa ta jihar Kano ta sanar da cewa za ta kaddamar da bincike bayan da ta samu wani korafi da wasu mutane dake zargin cewa majalisar ta kashe naira biliyan 3 zuwa 6 ba bisa ka’ida ba, cikin shekaru 3.

KU KARANTA KUMA: Zamu cigaba da bincikar asusun masarautar Kano – Muhyi Magaji

NAIJ.com ta ruwaito cewa jami’an kula da harkokin kudi na majalisar masarautar Kano dai sun bayyana a hedikwatar hukumar yaki da rashawa, a cewar Kwamrad Muhiyi Magaji, shugaban hukumar ta Kano, ya ce sun tattauna da ‘yan majalisar sun kuma baiwa hukumar hadin kai yadda ya kamata.

Da yake magana da manema labarai Walin Kano, Alhaji Bashir Wali, ya ce kudin da majalisar masarautar Kano ke dashi lokacin mai martaba Ado Bayero, naira biliyan 2 da miliyan 800.

Sai kuma Wali ya ce gabanin rasuwar Ado Bayero, an fitar da wasu kudade da yawansu ya kai naira miliyan 981 wanda aka biya ‘yan kwamitin gini gidajen Ado Bayero Royal City da ke Darmanawa.

Hakan yasa mai martaba sarkin Kano Mohammadu Sunusi na biyu ya gaji naira biliyan 1 da 893,000.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Sariki Sanusi ya shawarci shugabannin Najeriya da shugabanci na nagari a cikin wannan bidiyo

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiyar tsaro na farar hula ta bukaci a daure Sufeto Janar na ‘yan sanda

Kungiyar tsaro na farar hula ta bukaci a daure Sufeto Janar na ‘yan sanda

Kungiyar tsaro na farar hula ta bukaci a daure Sufeto Janar na ‘yan sanda
NAIJ.com
Mailfire view pixel