Akwai banbanci tsakanin likimo da barci – Inji Ganduje

Akwai banbanci tsakanin likimo da barci – Inji Ganduje

- Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya ce akwai banbanci tsakanin likimo da barci

- Masu hammayya dai na yawan sukar gwamnan da yin barci a wurin taruka

A baya-bayan nan hotunan gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje suka yi ta yawo a shafukan sada zumunta da ke nuna yadda Ganduje yake 'barci' a wuraren taruka.

Hakan ne yasa gwamnan kasa yin shiru har ya mayar da martani, a inda ya nemi rarrabe tsakanin tsaki da tsakuwa.

To amma hakan ya kara zafafa muhawara tsakanin bangaren gwamnan da ake kira Gandujiyya da kuma tsagin tsohon gwamna Rabi'u Kwankwaso da aka fi sani da Kwankwasiyya.

Akwai banbanci tsakanin likimo da barci – Inji Ganduje

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje

Kamar yadda NAIJ.com ke da labara, mabiya Kwankwasiyya sun ce likimo bacci ne, a inda magoya bayan Gandujiyya ke cewa mai basira ne kawai yake yin likimo.

KU KARANTA KUMA: An shawarci ya’yan jam’iyyar PDP da kar su halarci zaman kotu kan karar Sule Lamido

Wannan dai na nuna irin yadda rabuwar kai tsakanin 'yan jam'iyyar APC a jihar Kano ta kara tsanani.

Jim kadan dai bayan da gwamna Rabi'u Kwankwaso ya mika wa Abdullahi Ganduje mulki wanda tsohon mataimakinsa ne ake ta samun rarrabuwar kai.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga bidiyon da wani dan jam'iyyar APC ke bayyana nadamar kasancewa a cikin jam'iyyar sabili da masaloli daban-daban da APC fuskanta a hannun 'yan jam'iyyar

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Farfaɗo da martabar Arewa: Muhimman matakai guda 10 da ya dace yan Arewa su ɗauka – Shehu Sani

Farfaɗo da martabar Arewa: Muhimman matakai guda 10 da ya dace yan Arewa su ɗauka – Shehu Sani

Farfaɗo da martabar Arewa: Muhimman matakai guda 10 da ya dace yan Arewa su ɗauka – Shehu Sani
NAIJ.com
Mailfire view pixel