An shawarci ya’yan jam’iyyar PDP da kar su halarci zaman kotu kan karar Sule Lamido

An shawarci ya’yan jam’iyyar PDP da kar su halarci zaman kotu kan karar Sule Lamido

- An shawarci ya’yan jam’iyyar PDP da kar su halarci zaman kotu a cigaba da sauraron karar da gwamnan jihar Jigawa ke yiwa Alhaji Sule Lamido

- Mansur Ahmed ya bukaci a taya Lamido addua domin samun nasara a dukkan zaman kotun da za'a gabatar

Jam'iyyar PDP reshen Jihar Jigawa tana umartar dukkan ya'yanta da magoya baya da kar su halarci zaman kotu da za'a gabatar a safiyar ranar Alhamis, 4 ga watan Mayu, a cigaba da sauraron karar da gwamnan jihar Jigawa Badaru yake yiwa jagoran talakawa Alhaji Sule Lamido.

Sanarwar ta biyo bayan kokarin gujewa dukkan sharri da makarkashiya da kulli da nufin da ake da shi ko wani shiri na karkashin kasa domin bata suna ko cin zarafin sa da ake kokarin hada baki da wasu a yi.

KU KARANTA KUMA: Ka ji kudirin Gwamna Ayodele Fayose

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, sanarwar ta nemi masoya Alhaji Sule Lamido a ko'ina suke da su zauna a gidajen su, garuruwansu, domin yi masa adduar samun nasara a dukkan zaman kotun da za'a gabatar, da kuma Allah ya masa katanga da dukkan mai mugun nufi akansa, Allah ya mayar masa..

An shawarci ya’yan jam’iyyar PDP da kar su halarci zaman kotu kan karar Sule Lamido

Tsohon gwamnan jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido

Mai lura da yanar gizo na tsohon gwamnan jihar Jigawa, Mansur Ahmed ya shawarci masoya Alhaji Sule Lamido da su dauki wannan sanarwa da muhimmanci.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

'Yan uwar wadanda aka tsare a ofishin jami'in tsaro na farar hula, kali bayanin su a lokacin da suka ziyarce su

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Zan so diyar ciki na tayi harkar fim - Sadiq Ahmad

Dandalin Kannywood: Zan so diyar ciki na tayi harkar fim - Sadiq Ahmad

Dandalin Kannywood: Zan so diyar ciki na tayi harkar fim - Sadiq Ahmad
NAIJ.com
Mailfire view pixel