Za a mikar da sakamakon binciken Babachir da Oke a ranar Litinin

Za a mikar da sakamakon binciken Babachir da Oke a ranar Litinin

- Fadar shugaban kasa ta tabbatar da cewa kwamitin binciken manyan jami'an gwamnatin tarrayar Najeriya biyu da ake zargi da cin hanci da rashawa zata mika sakamakon binciken ga shugaba Buhari

- Akande ya ce kwamitin ta kammala aikin sa a ranar Laraba, 3 ga watan Mayu

Fadar shugaban kasa a ranar Laraba, 3 ga watan Mayu ta ce shugaban kwamitin gudanar da bincike kan dakataccen baban darekta na hukumar leken asiri ta kasa, Ambasada Ayo Oke, da kuma dakataccen sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal, zai yi mika sakamakon binciken ga shugaban kasa Muhammadu Buhari ranar Litinin, 8 ga watan Mayu.

NAIJ.com ta ruwaito cewa baban mai taimaka wa mataimakin shugaban kasar a kan harkokin watsa labarai, Mista Laolu Akande, ya bayyana hakan a wata sanarwa sakin layin daya ga 'yan jaridu.

Akande ya ce kwamitin da mataimakin shugaban kasar Yemi Osinbajo ya jagoranci ta shirya don kammala aiki a ranar Laraba, 3 ga watan Mayu.

KU KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ya karbi rahoton kwamitin gyara a harkokin zabe

Ama rahotannin a kafofin yada labarai na nuna cewa Babagana Monguno da kuma Babban Lauyan Tarayya, Abubakar Malami (SAN) a matsayin mambobin zai gabatar da sakamakon binciken a ranar Laraba, 3 ga watan Mayu.

Za a iya tuna cewa an kafa wannan kwamitin ne a ranar 19 ga watan Afrilu, aka kuma ba da umarnin mika rahoton ta a cikin kwanaki 14.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga bidiyon inda wani dan jam'iyyar APC mai mulki ya ce jam'iyyar na iya fadi a zabe mai zuwa a 2019

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Za’a sake ɗiban wasu sabbin hafsoshin rundunar Yansanda – Gwamnatin tarayya

Za’a sake ɗiban wasu sabbin hafsoshin rundunar Yansanda – Gwamnatin tarayya

Canji! Gwamnatin shugaba Buhari zata sake ɗiban sabbin hafsoshin Yansanda
NAIJ.com
Mailfire view pixel