Jam'iyyar PDP ta tafka babbar asara a jihar nan (Karanta)

Jam'iyyar PDP ta tafka babbar asara a jihar nan (Karanta)

- Ƴaƴan jam’iyar PDP sama da mutane 500 ne suka sauya sheƙa zuwa jam’iya mai mulki ta APC a ƙaramar hukumar Ikono dake jihar Akwa Iboma a ranar lahadin data gabata.

- Sauya sheƙar da mutanen sukayi a Ikono wacce take cibiyar al’ummar ƙabilar Ibibio na daga cikin sauya sheƙa dake damun jam’iyar PDP a jihar cikin ƴan kwanakin nan.

Cikin waɗanda suka sauya sheƙar a kwai tsofaffin kansiloli guda 4, da suka haɗa da Iboro Akpan,Samuel Etok, Ndifreke Essien, da kuma Jonathan Umana tsohon sakataren jam’iyar PDP na shiya da Dakta George Udo tsohon ma’aikacin jami’a da kuma Mista Victor Etefia wani mai harkar man fetur a jihar.

NAIJ.com ta samu labarin cewa da yake nasa jawabin tsohon Sanata mai wakiltar mazabar Akwa Ibom arewa maso yamma Aloysius Etok, ya bayyana jin ɗaɗinsa da sauya sheƙar, inda yace dukkanin cikakkun ƴan siyasa dake yankin yanzu suna cikin jam’iyar APC.

Jam'iyyar PDP ta tafka babbar asara a jihar nan (Karanta)

Jam'iyyar PDP ta tafka babbar asara a jihar nan (Karanta)

KU KARANTA: An kashe yar bautar saura kwana 2 ta gama

Etok ya tabbatarwa da Jam’iyar APC a jihar cewa zata samu ƙuri’a mai yawan gaske a zaɓen 2019, inda yaƙara da cewa lokacin da wasu mutane zasu zauna a gidan gwamnati su rubuta ƙuri’a ya wuce.

Sanatan ya ƙaryata iƙirarin da jam’iyar PDP tayi na cewa ta gina tituna har tsawon kilomita 250 a jihar.

A nata jawabin tsohuwar ƴar majalisar wakilai ta tarayya mai wakiltar mazaɓar Ikono/Ini , Misis Iquo Inyang ta yabawa waɗanda suka sauya sheƙar kan zaɓin da sukayi na rungumar canjin dake faruwa a ƙasa baki ɗaya.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiyar tsaro na farar hula ta bukaci a daure Sufeto Janar na ‘yan sanda

Kungiyar tsaro na farar hula ta bukaci a daure Sufeto Janar na ‘yan sanda

Kungiyar tsaro na farar hula ta bukaci a daure Sufeto Janar na ‘yan sanda
NAIJ.com
Mailfire view pixel