Batun Boko Haram ya mamaye taron yaki da ta’addanci na jami’ar California

Batun Boko Haram ya mamaye taron yaki da ta’addanci na jami’ar California

- Batun ta’addancin Boko Haram a Najeriya ne ta mamaye taron da aka gudanar a jami’ar California a kasar Amurka

- Farfesa Ashko Potato ya ce suna bincike akan abin da yasa mutane ke bijirewa bayan kuma a baya ana zaman lafiya dasu cikin al’umma

Batun ta’addancin Boko Haram a Najeriya shine ya mamaye taron da aka gudanar a jami’ar California, kan yaki da ta’addanci da ‘yan jaridu daga kasashen duniya suka halarta.

Ma’aikatar harkokin wajen Amurka, ta gayyato ‘yan jaridu daga sassa daban-daban na duniya, inda yanzu haka suke samun horo tare da rangadin jihohi daban-daban da jami’o’i da ma cibiyoyi na kasa da kasa a Amurka.

Batun tarzomar Boko Haram ce ta mamaye taron na jami’ar California, Farfesa Brandi Bangle, dake zama mataimakin daraktan sashen kimiyyar siyasar duniya a jami’ar da kuma ya yi tsokaci kan Boko Haram, ya ce daya daga cikin abin da ya kamata ai la’akari dashi shine idan ana batun ta’addanci irin na Boko Haram, to akida ce ke musu jagoranci.

Saboda haka ba za a maida hankali wajen amfani da karfin soji kadai ba, amma ya kuma kamata a maida hankali wajen yaki da ainihin akidar dake haddasa wannan tsatauran ra’ayi. Ya ce wasu daga cikin mayakan Boko Haram din na cikin kungiyar ne bisa tursasawa yayin da wasu kuma basu san ainihin abin da yasa suke ciki ba.

KU KARANTA KUMA: Jerin kungiyoyin da suke matsayin barazana ga tsaron kasa kamar yadda dillancin tsaron ya gabatar da

Farfesa Brandi wanda ya yabawa kokarin gwamnatin Najeriya bisa nuna da gaske take wajen yakar Boko Haram, amma ya yi gargadin amfani da karfin soji kadai ba zai kawo karshen matsalar ba a gaba daya, don haka akwai bukatar daukan karin wasu matakai.

Kamar yadda NAIJ.com ke da labara, Wani malami a jami’ar Farfesa Ashko Potato ya ce suna bincike akan abin da yasa mutane ke bijirewa bayan kuma a baya ana zaman lafiya dasu cikin al’umma, koda yake basu fara zurfafa bincike kan Boko Haram a Najeriya ba, saboda ba a gayyace suba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kali yadda aka bada belin shugaban 'yan Biafara Nnamdi Kanu

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin APC ta saki jerin hanyoyi da gadoji da ta kammala cikin shekaru 2 kacal

Gwamnatin APC ta saki jerin hanyoyi da gadoji da ta kammala cikin shekaru 2 kacal

Gwamnatin APC ta saki jerin hanyoyi da gadoji da ta kammala cikin shekaru 2 kacal
NAIJ.com
Mailfire view pixel