Zamu cigaba da bincikar asusun masarautar Kano – Muhyi Magaji

Zamu cigaba da bincikar asusun masarautar Kano – Muhyi Magaji

-Hukumar karbar koke koke da yaki da cin hanci da rashawa taci alwashin cigaba da bincikae masarautar Kano

-Shugaban Hukumar Muhuyi Magaji yace babu ruwansa da sulhun da aka yi tsakanin gwamna da Sarki

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano tace babu hannun hukumar EFCC a cikin binciken da suke yi daya shafi badakalar almubazzaranci da naira biliyan 6 a fadar masarautar jihar Kano. Inji rahoton Premium Times.

Shugaban hukumar Muhiyi Magaji Rimingado ne ya bayyana ma kamfanin dillancin labaru, NAN, a ranar Talata 2 ga watan Mayu, inda ya musanta labarin da ake yadawa na cewa wai EFCC sun shiga cikin binciken.

KU KARANTA: Jerin kamfanunuwa 5 da suka baiwa Babachir cin hancin naira miliyan 507

Muhiyi yace “Gaskiya ne na gana da shugaban EFCC, Ibrahim Magu a satin data gabata, amma batutuwan da suka shafi hukumar muka tattauna, bamu mika musu ragamar binciken masarautar Kano ba, ta yaya za’a ce wai jami’an EFCC sun dira fada?”

Zamu cigaba da bincikar asusun masarautar Kano – Muhyi Magaji

Muhyi Magaji

Da aka tambaye shi game da sulhu da aka ce gwamnonin Arewa sun yi tsakanin gwamna Abdullahi Ganduje da Sarki Muhammadu Sunusi, Muhiyi Magaji ya shaida ma majiyar NAIJ.com ba ruwansa da wannan.

“Asali ba gwamnatin jihar ta sanya mu fara gudanar da binciken ba, don haka ba tad a hurumin dakatar damu, saboda dokokin hukumar yaki da cin hanci na jihar Kanona sun bamu daman cin gashin kan mu, don haka babu wanda zai juya mu.”

Zamu cigaba da bincikar asusun masarautar Kano – Muhyi Magaji

Sarkin Kano

“Muna amfani ne korafe korafe da muka samu daga jama’a, don haka zamu cigaba da gudanar da binciken zargin almubazzarancin kudade a fadar masarautar Kano.” Inji Muhiyi Magaji

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Sarkin Kano yayi muhimmin batu, kalla

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dubi jerin hanyoyi da gadoji da gwamnatin APC ta ce ta kammala cikin shekaru 2

Dubi jerin hanyoyi da gadoji da gwamnatin APC ta ce ta kammala cikin shekaru 2

Gwamnatin APC ta saki jerin hanyoyi da gadoji da ta kammala cikin shekaru 2 kacal
NAIJ.com
Mailfire view pixel