Toh fa: Ko ka san kasar da tafi hatsari a aikin jarida a duniya?

Toh fa: Ko ka san kasar da tafi hatsari a aikin jarida a duniya?

- Yau ce ranar da aka ware a matsayin ranar kare hakkin ‘yan jaridu ta duniya

- Kungiyar kare hakkokin 'yan jaridu ta bayyana kasar Mexico ne mafi hadari ga ‘yan jaridu

Yau ce Majalisar Dinkin Duniya, MDD ta ware a matsayin ranar kare hakkin ‘yan jaridu ta duniya, inda masana da ma’aikata ke nazari irin ci gaban da aka samu da kuma akasin haka.

Kungiyar da ke kare hakkokin 'yan jaridu ta bayyana kasar Mexico a matsayin mafi hadari ga ‘yan jaridu, ganin yadda aka kashe sama da mutane 50 a cikin shekaru 7.

KU KARANTA KUMA: Jerin kamfanunuwa 5 da suka baiwa Babachir cin hancin naira miliyan 507

Bincike ya nuna cewar gwamnatoci da kungiyoyin 'yan siyasa da kuma 'yan ta’adda ke kai hari ko dirar mikiya kan 'yan jaridun dan hana fadawa mutane gaskiya.

Kungiyar ta bayyana wasu kasashen Afirka da aikin jarida ke fuskantar hadari da suka hada da Masar da Tunisia da Tanzania da Kamaru da Jamhuriyar Dimokiradiyar Congo da kuma Burundi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga bidiyo inda hukumar EFCC ta gurfanar da tsohon babban daraktan NNPC Andrew Yakubu a kotu kan zargin cin hanci da rashawa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Abubuwan da Abacha yaso yi washe-garin ranar da ya rasu a June 1998

Abubuwan da Abacha yaso yi washe-garin ranar da ya rasu a June 1998

Abubuwan da Abacha yaso yi washe-garin ranar da ya rasu a 1998
NAIJ.com
Mailfire view pixel