Jerin kamfanunuwa 5 da suka baiwa Babachir cin hancin naira miliyan 507

Jerin kamfanunuwa 5 da suka baiwa Babachir cin hancin naira miliyan 507

-Kwamitin majalisar dattawa ta bankado kamfanunuwa da suka baiwa Babachir cin hanci

-Dakataccen sakataren gwamnatin tarayya Babachir ya sake shiga matsala

Kwamitin majalisar dattawa dake binciken badakalar yankan ciyawa da ake zargin Babachir David Lawal karkashin shugabancin Sanata Shehu Sani ta bankado yadda Babachir yayi amfani da wasu kamfanunuwa wajen satar kudaden sake tsugunnar da mutanen da rikicin Boko Haram ya shafa a yankin Arewa maso gabas.

Kwamitin ta bayyana haka ne cikin rahoton sakamakon binciken da ta gudanar, wanda ta mika ma majalisar a ranar Laraba 3 ga watan Mayu.

KU KARANTA: Majalisar dattawa ta tabbatar da sababbin ministoci guda 2 Majalisar dattawa ta tabbatar da sababbin ministoci guda 2

Shugaban kwamitin, Sanata Shehu Sani ya bayyana cewar “A yayin binciken mu, mun gano Rholavision ta karbi cin hanci daga hannun yan kwangila ta asusun bankin kamfanin dake Ecobank mai lamba 0182001809.”

Jerin kamfanunuwa 5 da suka baiwa Babachir cin hancin naira miliyan 507

Kwamitin Shehu Sani

1- Rahoton yace, a tsakanin ranar 29 ga watan Maris zuwa 20 ga watan Afrilu na shekarar 2016 wani kamfani mai suna JOSMON technologies daya samu kwangila har guda biyu na kusan miliyan 530 ya sanya naira miliyan 317 cikin asusun kamfanin Babachir David Lawal ta hanyar aikawa da kudaden ha sau 23.

2- Haka zalika, a ranar 8 ga watan Agustan 2016 wata kamfani mai suna JMI Global technologies da ta samu kwangila guda 8 daya kai na naira kiliyan 199, amma sai ta sanya naira miliyan 30 cikin asusun bankin Rholavision kamfanin Babachir dake Bankin Ecobank daga wani asusun Zenith Bank mai lamba 114357188.

Jerin kamfanunuwa 5 da suka baiwa Babachir cin hancin naira miliyan 507

Babachir

3- Sai wani kamfani mai suna Messers Adamawa Borehole and Drilling Company daya samu kwangilar gyaran azuzuwa 18 a makarantar sakandari ta yan mata dake Yeskule a garin Michika da aka biya naira miliyan 54.8, shima kamfanin ya sanya ma Babachir naira miliyan 18.3 a asusun bankin.

4- Shima wani kamfani mai suna Barde Brothers multi-service limited da suka samu kwangilar gyaran azuzuwa, kuma aka biya su naira miliyan 145.6 sun biya kamfanin Rholavision na Babachir naira miliyan 84 a tsakanin 7 ga watan Yuli zuwa 9 ga watan Satumbar2016

5- Kamfanin Yuby Ventures Limited suma da ta samu kwangilar gina azuzuwa 15 a makarantar Firamari na Hausari a Adamawa ta biya kamfanin Babachir naira miliyan 58.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Rikita rikitan EFCC da barayin gwamnati

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Canji! Gwamnatin shugaba Buhari zata sake ɗiban sabbin hafsoshin Yansanda

Canji! Gwamnatin shugaba Buhari zata sake ɗiban sabbin hafsoshin Yansanda

Canji! Gwamnatin shugaba Buhari zata sake ɗiban sabbin hafsoshin Yansanda
NAIJ.com
Mailfire view pixel