Majalisar dattawa ta tabbatar da sababbin ministoci guda 2

Majalisar dattawa ta tabbatar da sababbin ministoci guda 2

-Daga karshe majalisae dattawa ta tantance sabbin ministocin da Buhari ya aike mata

-Majalisar ta tabbatar da Farfesa Steven Ocheni da Suleiman Zarma

Majalisar dattawa ta tabbatar da nadin sabbin ministoci guda biyu da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aika mata a ranar Laraba 3 ga watan Mayu.

Sabbin ministocin sun hada da Steven Ocheni daga jihar Kogi da kuma Suleiman Zarma daga jihar Gombe, wanda ake sa ran zasu maye gurbin marigayi minista Ocholi daga jihar Kogi da kuma tsohuwar minista Amina Muhammed data samu cigaba zuwa majalisar dinkin duniya.

KU KARANTA: Babachir ya karɓi na goro daga hannun yan kwangila

NAIJ.com ta ruwaito hukumar jami’ar jihar Kogi daga inda Steven Ocheni ya fito ta wanke shi daga zarge zargen aikata kowane irin laifi a jami’ar.

Majalisar dattawa ta tabbatar da sababbin ministoci guda 2

Farfesa Steven Ocheni

Kaakakin jami’ar KSU ne ya sanar da haka a ranar Talata 2 ga watan Mayu inda yace hukumar jami’ar tabi dukkanin hanyoyin da suka dace wajen nada Steven mukamin farfesa, kamar yadda tsarin yake a dukkanin jami’o’in kasar nan.

Majalisar dattawa ta tabbatar da sababbin ministoci guda 2

Suleiman Zarma

Sanarwar ta kara da fadin tun a shekarar 2014 ne hukumar jami’ar ta tabbatar da Steven Ocheni a matsayin farfesa.

Ga bidiyon nan:

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kalli ra'ayin yan Najeriya game da majalisar dattawa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile faruwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma

Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile faruwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma

Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile afkuwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma
NAIJ.com
Mailfire view pixel