Shugaban kasan Austria yayi kira ga dukkan matan kasar su sanya hijabi na kwana daya

Shugaban kasan Austria yayi kira ga dukkan matan kasar su sanya hijabi na kwana daya

-Shugaban kasar Turai ya goyi bayan sanya hijabi

-Yace kowa na da hakkin sanya abinda ya ga dama

Shugaba kasar Austria, Alexander Van der Bellen, yayi kira ga dukkan matan kasar Austria sun sanya hijabi na kwana daya domin nuna goyon baya ga matan musulman da ke fuskantan kalubale a kasar domin sanya hijabai.

Jaridar Indepenent ta bada rahoton cewa shugaban kasan yace: “ Hakkin kowace mace ne ta sanya abinda ta ga dama, wannan shine ra’ayi na akan al’amarin.”

“Kuma ba matan musulmai kadai ba, dukkan mata zasu iya sanya gyale, kuma idan wannan cin mutuncin masu sanya hijabi ya cigaba, zamu umurci dukkan mata su sanya gyale domin nuna goyon baya ga musulmai masu sanyawa saboda biyayya ga addininsu.”

Shugaba kasan Austria yayi kira ga dukkan matan kasar su sanya hijabi na kwana daya

Shugaba kasan Austria yayi kira ga dukkan matan kasar su sanya hijabi na kwana daya

Van der Bellen, wanda ya samu nasarar zaben shugaban kasan ya bayyana wannan ne lokacin da yake amsa tambayar wata daliba da ta tambayeshi akan zancen hijabi.

KU KARANTA: An hallaka yar bautar kasa a Abuja

A wata jawabi kuma, Van der Bellen, ya masu wakilatar musulmai a kasar Austria suyi bayanai filla-filla kan abubuwan da mutane ke jinginawa addinin musulunci.

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnati ta karrama wadanda suka bada gudummawa wajen habakar kasuwanci a 2016-
2017

Gwamnati ta karrama wadanda suka bada gudummawa wajen habakar kasuwanci a 2016- 2017

Gwamnati ta karrama wadanda suka bada gudummawa wajen habakar kasuwanci a 2016/2017
NAIJ.com
Mailfire view pixel