Kaunar da nakeyiwa Yesu ta kaini ga shiga addinin musulunci

Kaunar da nakeyiwa Yesu ta kaini ga shiga addinin musulunci

- Zama da Musulmai yasa Sara Price yar yawon bude idon kasar Australia ta musulunta

- Mummunar fahimta wa addinin musulunci kesa a kyamaceshi

A ma'anarsa na kalma ‘Mika wuya don da'a ga Allah ’, Musulunci addini ne da ake alaqantashi da dabi'u miyagu dayawa ta hanyoyin yada labarai a ba akan gaskiya ba.

Toh tayaya za'ayi gogargiyar mai ilimi mai yawon bude ido matashiya yar kasar Australian ta zami ta zama musulma dukda nuna ci bayansa da akeyi?

Na fuskanci maganganu da tsangwama sosai daga mutane,gurin aiki da sauransu sakamakon sakamakon wannan rawargani da naayi.

NAIJ.com ta tabbatarda Abubuwan da suka haifar da sanadin musulunta ta na dayawa, a fadarta:

''Daga mafi girma akwai tafiya ta zuwa Malaysia nan ne ginshikin musulunta ta, anan ne idona ya bude zuwaga daidai a abubuwan da nakewa bahaguwar fahimta gameda addinin musulunci. a tunani na a da, musulmai ba wayaryu bane,kuma matan musulmi na cikin takura.

''Amma ina, sabanin hakan na gani a garin nan. na ga abubuwa dayawa masu ban sha'awa a masallatai da gidajen musulmai dake tabbatar da ado da ban sha'awar adiinin, har sai da naji kamar ga sabon gida nan na samu saboda nutsuwa.

''Duka abubuwan da na gani ba komai suka kareni dashi ba face tabbatar mini da kadai takar Allah madaukaki.

''Ni yar gani kashenin addinin kiristanci ce a da kafin na musulunta,kuma karfin imani na a addinin gurin bin shiriyarwarsa ne ya kaini ga musulunci. tabbas addinin kiristanci na daga addinan mafi kusa da musulunci. ya tabbata a musulunci cewa annabi Muhammad SAW ya hana musgunawa kiristoci da sauran addinai,yayi umarni da a kyautata musu, da sauransu.''

Abinda zan iya cewa gameda bambanci tsakanin addinan biyu,shine musulunci na tabbatar da matsayin Yesu a annabi ba abin bauta ba da kuma tabbatarda kadaituwar Allah a bauta.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Farfaɗo da martabar Arewa: Muhimman matakai guda 10 da ya dace yan Arewa su ɗauka – Shehu Sani

Farfaɗo da martabar Arewa: Muhimman matakai guda 10 da ya dace yan Arewa su ɗauka – Shehu Sani

Farfaɗo da martabar Arewa: Muhimman matakai guda 10 da ya dace yan Arewa su ɗauka – Shehu Sani
NAIJ.com
Mailfire view pixel