2019 : Ka ji kudirin Gwamna Ayodele Fayose

2019 : Ka ji kudirin Gwamna Ayodele Fayose

– Gwamnan Jihar Ekiti ya bayyana niyyar sa na shekarar 2019

– Ayodele Fayose yace ba zai nemi kujerar Sanata ba

– Gwamnan yace yanzu kuma hutawa zai je yayi

Gwamna Fayose yace ba zai nemi kujerar Sanata idan ya kammala wa’adin sa ba.

Fayose ya saba caccakar shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Gwamnan dai yace ba kujera da yake nema a kasar.

2019: Ka ji kudirin Gwamna Ayodele Fayose

Gwamnan Jihar Ekiti Ayodele Fayose

Gwamnan Jihar Ekiti Ayodele Peter Fayose ya bayyana cewa bai da wata niyya ta tsayawa takara a zabe mai zuwa 2019. Gwamna Fayose dai zai kammala wa’adin sa a shekara mai zuwa, dama can ya taba rike kujerar Gwamnan a baya.

KU KARANTA: Sanata Shehu Sani zai kara da Gwamna El-Rufai

2019 : Ka ji kudirin Gwamna Ayodele Fayose

Gwamna Fayose wajen yakin zabe

Fayose yace idan har ya bar Ofis abin da ke gaban sa shi ne ganin talaka ya ji dadi a Najeriya. Ayo Fayose ya kira Jama’a a Garin Ado-Ekiti cewa su yi maza su nemi katin zabe idan har ba su da shi.

Ana ta rade-radin cewa jikin Shugaba Buhari kullum kara tabarbarewa yake yi don yanzu haka bai halarci taron Majalisar ba sai kuma gas hi yanzu dai tsinci wasu hotunan takarar shugaba Buhari a zabe mai zuwa a Birnin Makurdi.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Zanga-zangar Biyafara a Garin Abuja

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila
NAIJ.com
Mailfire view pixel