Rikicin kudancin Kaduna: El-Rufai ya dage hana zirga-zirga a kananan hukumomi 2

Rikicin kudancin Kaduna: El-Rufai ya dage hana zirga-zirga a kananan hukumomi 2

- Gwamna Nasir El-Rufai yayi umarni da a kama duk wadanda ake zargin suna haddasa rikicin kudancin kaduna

- Gwamnatin jihar Kaduna ta dage hana hana zirga-zirgar da ta sanya wa karamomin hukumomi biyu na jahar

Kananan hukumomin biyu sune Jema'a da Kaura. hana zirga zirga da aka sanya a Zangon Kataf ya gabatu da dagewa, hakan kuwa ya auku ne sati biyu bayan da hukumar sojojin najeriya suka samar da operation ‘Harbin Kunama da nufin magance rikice-rikicen yankin kudancin jihar kadunan.

NAIJ.com ta nakalto a wani jawabin na Mai magana da yawun Gwamna Nasir El-Rufai’s, Samuel Aruwan, yace an dage hana zirgazirgar da akayi a kananan hukumomin biyu a Disamba 2016 da kuma farkon shekarar nan bayan sabon rikici da ya bijiro a sakamakon shawarwarin hukumar tsaro (SS) ta jihar.

KU KARANTA : Shugaba Buhari bazai iya juriyar karin shekaru 4 ba, inji jigon jam’iyyar PDP

A wani daga bangare na shawarwarin da NAIJ.com ta sake nakaltowa shine, “taron yau ya ya samu kuma ya waiwayi rahotanni daga hukumomin tsaro dake nuna samun cigaba a harkar tsaro. sakamakon haka hukumar ta zabi shawarar dage hana zirgazirgar da aka sanya ba tareda bata lokaci ba.

“Hukumar SS ta kara da cewa dukkanin mazauna yankin zasu ribaci damarmaki da hukumar tsaron zasu samar domin cigabar wanzuwar zama lafiya a yankin."

Taron hukumomin tsaron, da El-Rufaiya jagoranta, ya kunshi komandan 1 Division Garrison,Na sojojin Najeriya, Brig-Gen Ismaila Isa; wakilin Commandant, Wakilin sojojin Ruwa daga Nigerian Navy School of Armament, Capt SM Ochidi; da kwamishinan yansanda, Mr. Agyole Abeh, da shugaban jami'an tsaron jihar.

Ku biyomu a facebook https://www.facebook.com/naijcomhausa/

Kubiyomu a twitter https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile afkuwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma

Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile afkuwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma

Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile afkuwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma
NAIJ.com
Mailfire view pixel